Yakim Gaza: Saudiya Ta Hana Dr Gumi Yin Aikin Hajjin 2025
Hukumomon Saudi Arabiya sun hana shaharraren Malamin Nigeria Dr Ahmad Mahmud Gumi shiga kasar domin gudanar da aikin hajjin wannan shekara ta 2025
Masharhanta dai sun alakanta wannnan mataki da aka dauka a kan Dr Gumi da matsayin da ya dauka na tausayawa Palasdinawa kan irin kisan kare dangi da Israila ke musu tare da sukan hukumomon kasashen larabawa da sauran hukumomo ma duniya wajen gaza daukar matakin da ya dace dan tsaida yakim.
A cikin wani ba yani da ya wallafa ta kafar sada zumunta, Dr Gumi yace hana shi shiga Saudiya na da alaka da irin matsayinsa kan al”amuran siyasar duniya.
Ya ce duk da an bashi biza ta shiga Saudiya amma bayan ya sauka a Jidda sai aka ce ya komo Nigeria.
Ya kuma godewa hukumomon Nigeria da suka yi alkawarin bin diddigin wannan matsala.
Adaidai lokacin da Israila ke kara kaimi wajen cigaba da kisan kare dangi a Gazza, tare da goyon bayan Amuruka, ita kuma kasar ta Saudiya fa wasu kasashen Larabawa sun shagala da kara zuba Jarin biliyoyin Daloli a kasar ta Amuruka.
I zuwa yanzu Israila ta kashe Palasdinawa sama da 56,000 a yakim da ta dau tsawon sama da shekara guda tana yi da Palasdinawa.




