By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: TAI da Baykar na Turkiyya na daga cikin manyan kamfanonin ƙera jiragen sama 50 na duniya
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > TAI da Baykar na Turkiyya na daga cikin manyan kamfanonin ƙera jiragen sama 50 na duniya
International News

TAI da Baykar na Turkiyya na daga cikin manyan kamfanonin ƙera jiragen sama 50 na duniya

Attajdid
Last updated: 2024/11/12 at 5:11 PM
Attajdid Published November 12, 2024
Share
SHARE

Kamfanonin ƙera Jiragen Sama na Turkiyya TAI da Baykar sun shiga cikin jerin manyan kamfanoni 50 mafi girma a duniya bisa kudaɗen shigarsu na shekarar 2023, a cewar rahoton FlightGlobal.

 

Sashen kula da sararin samaniyar Turkiyya ya samu wani gagarumin ci gaba mai cike da tarihi, inda kamfanonin ƙasar biyu da ke ƙera jiragen sama wato TAI da Baykar suka shiga jerin manyan kamfanonin jiragen sama 50 na duniya, bisa ga kiɗiddigar kuɗaɗen shigarsu ta shekarar 2023 wadda hukumar leƙen asiri ta Counterpoint Market na FlightGlobal ta fitar.

 

Kamfanin TAI na matsayi na 38, inda ya ba da rahoton samun dala biliyan 2.67 na kuɗaɗen shigarsa, yayin da Baykar ke a matsayi na 49 da dala biliyan 1.8.

 

Matsayin TAI na 38 na nuna irin ci gaba da ya ke samu, inda ya samar jiragen masu saukar angulu ƙirar ANKA lll, da HURJET da kuma jirgin yaƙi na KAAN.

 

TAI ya fice wajen samar da manyan fasahohi na zamanin tare da ci gaba a fannin bincike, da kuma mayar da hankali wajen fitarwa da kuma samar da tsarin samfuran fasahohi ga manyan kamfanonin jiragen sama.

 

Haɗin gwiwar kamfanin tare da fitattun kamfanoni a harkar kusawancin jiragen sama masu zaman kansu da na sojoji a duniya ya karfafa masa yin fice.

 

Baya ga manyan samfuran kayayyakin tsaro da yake samarwa, haɗin gwiwar TAI da sauran kamfanoni masu zaman kansu a fannin jiragen sama ya ƙarfafa rawar da ya ke takawa a matsayin mai mahimmanci wajen samar da manyan fasahohi.

 

Matsayin Baykar na farko a jerin

 

Baykar, wani babban kamfani ne a fannin kasuwanin kera jirage marasa matuƙi (UAV), yana matsayi na 49 a jerin inda kudaden shigar da ya samu a 2023 ya kai dala biliyan 1.8.

Ya yi fice a samfurin jirginsa na Bayraktar TB2, kazalika kamfanin ya yi suna wajen fitar da jiragen yaki marasa matuki a duniya, tare da fasaharsa da ake buƙata a duk faɗin duniya.

 

Baykar ya sanya hannu kan yarjejeniyar fitar da kayayyakinsu zuwa kasashe 35 kan samar da jiragensa ƙirar Bayraktar TB2 da Bayraktar AKINCI UAVsƙ

 

Fiye da kashi 90 cikin 100 na kudaɗen da kamfanin ya samu ya fito ne daga fitar da kayayyakinsa zuwa ƙasashen duniya, Baykar ba kawai ya tsaya wajen fayyace fannin tsaron Tukiyya ba ne, yana riƙe da matsayinsa na babban kamfanin da ke fitar da kayyaykin tsaro na ƙasar mai fitar a tsawon shekaru uku a jere.

 

Dukka kamfanonin biyu, TAI da Baykar suna ci gaba da saka hannun jari a sabbin fasahohi.

 

TAI yana ci gaba da ƙera jiragen yakinsa na KAAN, yayin da Baykar ke mai da hankali wajen samar da jiragen yaki marasa matuka ƙirar Bayraktar TB3, da jirgin ruwa mai saukar ungulu ƙirar UAV, da kuma Bayraktar Kizilelma da ake sa rai samarwa wato jirgin yaki na sama na farko na Turkiyya.

 

Ci gaba a kasuwanin duniya

 

Matsayin dai, ya sanya TAI da Baykar a cikin jerin manyan kamfanoni kamar Boeing da Airbus, waɗanda bi da bi suke kan gaba a jerin kudaɗen shigar kamfanonin ƙera jiragen samana duniya da dala biliyan 77.8 da kuma dala biliyan 70.8.

 

Manyan kamfanonin da ke kan gaba a jerin sun fito ne daga Amurka da ƙasashen Turai, yanayin da ke nuni da irin rinjayen da kamfanonin Amurka da na Turai a fannin sararin samaniya, musamman waɗanda suka mayar da hankali wajen samar da fasahohin tsaro da na farar hula.

 

A bana dai, manyan kamfanoni irin su RTX, da Lockheed Martin, da Northrop Grumman suna ci gaba da taka muhimmiyar rawa a fannin masana’antar tsaron Amurka a duniya.

 

Ko da yake, bayyanar kamfanoni irin su Baykar da TAI na nuna sauyin da ake samu a wannan ɓangare, inda kamfanonin waɗanda ba na ƙasashen Yammacin Turai ba suke shiga jerin da kamfanonin ƙasashen Yamma suka mamaye.

 

Mai Rahoto

Mujahid Muhammad Tasiu

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid November 12, 2024 November 12, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Kotu Ta Tasa keyar Wani  Alƙalin Bogi Gidan Gyaran Hali a Kano

Attajdid Attajdid September 6, 2024
Gina Jamiyya Ne A Gabanmu Ba Zaɓar Wanda Zai Yi Takarar Ba – ADC
Jigawa Commence Distribution of FG Palliative of 59,000 Bags of Rice, Maize Others
Yahudawan Sahyoniyya Sun Kashe Saban Shugaban Hezbollah
Bakon Ya Sami Tarba Mai Girma Gwamnan Kano
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?