Manchester United ta bude wasanninta na Firimiya da nasara a kan kungiyar Fulham. United ta samu nasara ne da ci 1-0 sakamakon kwallon da sabon ‘dan wasanta Joshua Zirkzee ya jefa mata a mintuna 87 da fara wasan bayan barin da ta yi a dama a gaban ragar Fulham. Wannan shi ne wasan farko na bude gasar Firimiya na wannan sabuwar kaka.
📷 Reuters




