By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan N712 domin mayar da Filin Jirgin Sama na MMIA na Legas sahun gaba a duniya
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan N712 domin mayar da Filin Jirgin Sama na MMIA na Legas sahun gaba a duniya
News

Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan N712 domin mayar da Filin Jirgin Sama na MMIA na Legas sahun gaba a duniya

Attajdid
Last updated: 2025/08/04 at 10:43 AM
Attajdid Published August 4, 2025
Share
SHARE

Gwamnatin Tarayya ta ware Naira biliyan N712 domin mayar da Filin Jirgin Sama na MMIA na Legas sahun gaba a duniya.

 

Gwamnatin tarayya tace Za ta mayar da filin jirgin sama na Legas cibiyar zirga-zirgar jiragen sama ta Yammacin Afirka bayan shekaru biyu da gyara.

 

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa gyaran filin jirgin sama na Murtala Muhammed (MMIA) da ke Legas da zai ci kimanin naira biliyan 712.3 zai mayar da filin jirgin zuwa sahun gaba a duniya.

 

Bayan kammala aikin cikin shekaru biyu, ana sa ran filin jirgin zai zama cibiyar zirga-zirgar jiragen sama a Yammacin Afirka.

Ana sa ran za a dauki nauyin aikin gaba daya daga shirin Nan na sabunta Fata da aiyukan more rayuwa, Wanda shugaban kasa ya fito dashi.

 

Ministan Sufurin Jiragen Sama da Ci gaban Sararin Samaniya, Festus Keyamo, da Daraktar Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN), Hajiya Olubunmi Kuku, sun yi karin bayani game da aikin a karshen mako, wanda Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da shi makon jiya.

 

Wannan gyara zai hada da canza fasalin ginin Terminal 1 gaba daya, wanda aka kaddamar tun shekarar 1979, da kuma sake tsara Terminal 2 wanda aka fara amfani da shi a karshen mulkin shugaba Buhari.

 

Haka kuma, za a yi wa wuraren ajiye jiragen sama, wuraren ajiye motoci, hanyoyin shiga da fita da kuma sashe na kasa da kasa na filin jirgin sabbin gyare-gyare.

 

filin jirgi, wanda shi ne mafi yawan zirga-zirga a Najeriya, na dauke da kashi 67% na dukkan fasinjojin da ke tashi daga cikin kasar.

 

Hajiya Kuku ta bayyana aikin a matsayin wani babban shiri da zai mayar da MMIA zuwa matakin da zai kai daidaito da ingantattun filayen jirgin sama na duniya.

 

Ta ce aikin yana da hangen nesa, domin zai shafi kusan dukkanin muhimman bangarori na filin jirgin.

 

Keyamo ya bukaci wadanda ke sukar aikin da su nemi karin ilimi game da yadda ake kashe kudade wajen gina manyan filayen jiragen sama a duniya kafin su yi sharhi mara tushe.

 

Haka zalika, mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Tope Ajayi, da ya wallafa a shafinsa na X ya bayyana cewa irin wannan sabuntawa na filayen jirgin sama na kasa da kasa yana faruwa a sassan duniya.

 

Hajiya Kuku ta bayyana wasu daga cikin ribar aikin da suka hada da Gyaran sashen wajen ginin, da cikin ginin, ciki har da tsarin bututun ruwa, lantarki domin su daidaita da ka’idodin duniya.

 

Haka kuma, gwamnati za ta gina sabuwar hanyar mota da za ta kasance ta zamani da sauki, domin saukaka cunkoso da bunkasa jin dadin masu zuwa filin jirgin.

 

Wani bangare mai muhimmanci na shirin shi ne gyaran fili gaban ginin, domin kara maraba da saukar baki cikin kwarewa da nuna al’adun kasa.

 

Ta ce za a tsara central square da ke gaban filin jirgin yadda zai kasance abin alfahari ga kasa kuma ya zama kyakkyawan hoto na farko ga masu zuwa Najeriya.

Shugabar FAAN ta bukaci hadin kai da fahimtar dukkan masu ruwa da tsaki da fasinjoji yayin da aikin ke gudana.

 

 

Mai Rahoto

Nura Abubakar Musa

You Might Also Like

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

UNICEF Urges Media to Advocate for Increased Water, Sanitation, and Hygiene Budget.

Attajdid August 4, 2025 August 4, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
International News

AN KASHE MUTANE 39,897 A GAZA TUN DAGA 7 GA WATAN OKTOBA NA SHEKARAR 2023 ZUWA YAU.

Attajdid Attajdid August 12, 2024
GAME DA HUKUNCIN DONALD TRUMP AKAN NAJERIYA
To ease inflation, FG proposes temporary Zero-Duty on food imports.
SULHUN TSAGAITA WUTA TSAKANIN HAMAS DA ISRA’ILA – WA YA CIMMA MANUFOFIN SA, WAYE BAI YI BA?
Sakon ‘Yan Gwagwarmayar ‘Yantar Da Kasar   Palastinu Na Duniya 🇵🇸 Da Kasar Labanon
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?