By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Rundunar ‘Yan Sandan Nigeria Ta Janye Jami’anta Daga Hedikwatar Kananan Hukumomin a Jahar Rivers
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Rundunar ‘Yan Sandan Nigeria Ta Janye Jami’anta Daga Hedikwatar Kananan Hukumomin a Jahar Rivers
News

Rundunar ‘Yan Sandan Nigeria Ta Janye Jami’anta Daga Hedikwatar Kananan Hukumomin a Jahar Rivers

Attajdid
Last updated: 2024/10/08 at 6:50 AM
Attajdid Published October 8, 2024
Share
SHARE

Rundunar ‘yan sandar jihar Rivers ta janye jami’anta daga dukkan sakatariyar ƙananan hukumomi 23 da ke jihar, hakan na zuwa ne bayan kammala zaɓen ƙananan hukumomin tare da rantsar da wadanda suka yi nasara.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Rundunar ‘yansandar, Grace Iringe-Koko , ta fitar da safiyar yau Litinin ta tabbatar da hakan.

Ta ce kwamishinan ‘yansanda na jihar ya bayar da umarnin ne ƙarƙashin umarnin Sifeto Janar, Kayode Egbetokun, wanda ya umarci a janye jami’an da ke samar da tsaro a dukkan hedikwatar ƙananan hukumomin jihar nan take.

Jam’iyar APP ce ta samu nasarar lashe zaɓen ƙananan hukumomi 22 a cikin 23, yayin da jam’iyar AA ta samu nasarar lashe zaɓen ƙaramar hukumar, Etche.

Jami’an ‘yansandan dai sun ƙarɓe iko da hedikwatar ƙananan hukumomin jihar Rivers a watan Yuni sakamakon rashin fahimta da ta shiga tsakanin Kantomomi masu goyon bayan gwamnan jihar mai ci Siminalayi Fubara da kuma tsoffin shugabannin ƙananan hukumomi na gwamnatin da ta gabata da ke goyon bayan tsohon gwamnan jihar kuma ministan Abuja, Nyesom Wike.

Gwamna Siminalayi Fubara na takun saƙa da tsohon uban gidansa, ministan Abuja, Nyesom Wike, inda kowanensu ke son samun rinjaye a siyasance a jihar.

Rikicin ya sanya yaran gwamna Fubara barin jam’iyar PDP, inda suka yi takara a jam’iyar APP.

Mai rahoto;

Salihu Garba. A

At-tajdid News.

You Might Also Like

Speakers Forum Congratulates Kwara, Katsina Speakers for Securing Governorship, Senate Tickets

Jigawa Governor: Our One Million Votes for Tinubu Are Non-Negotiable , Irreversible

Governor Namadi Affirmed as APC Jigawa State Gubernatorial Candidate for 2027

APC Primaries: Jigawa Speaker Retains Ticket Unopposed

Nursing Mother Inmate Freed as Jigawa NLC Women’s Wing Clears Her Court Fines

Attajdid October 8, 2024 October 8, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
International News

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

Attajdid Attajdid November 12, 2025
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci sojojin Najeriya su ƙara jajircewa wajen yaƙar matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar nan.
Netanyahu Yana Tsoran Za a Kawo Masa Hari Daga Lebanon 
Zaben Kananan Hukumomin Jihar Kano:
WANENE MUHAMMED ALBASHIR SABON FIRA-MINISTAN SYRIA
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?