Matatar mai ta Ɗangote zata fara jigilar man fetur kyauta daga ranar Litinin mai zuwa,
Mai magana da yawun rukunin kamfanin Ɗangote, Anthony Chiejina, shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda yace shirin zai fara ne daga jihohin Kudu maso Yamma, Abuja, Kwara, Delta, Rivers da Edo.
Ya ƙara da cewa matatar man ta riga ta rage farashin man fetur zuwa Naira 841 a kowace lita a Lagos da sauran jihohin Kudu maso yamma, yayin da a Abuja, Edo, Kwara, Rivers da Delta za a sayar da shi kan Naira 851 a kowace lita.
A baya dai an shirya fara wannan shiri tun watan Agusta, amma aka samu tsaiko saboda matsalolin sufuri daga kasar China.
Rahotanni sun ce anyi tanadin motocin dakon mai sama da 1,000 da za su fara aikin rabon, kuma ana sa ran ƙarin jihohi za su shiga cikin shirin nan gaba kaɗan yayin da ƙarin manyan motocin ke iso wa Najeriya.




