By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Abin da ya Kamata ku Sani Kan ƙungiyar da Putin ke Karɓar Baƙuncinta: BRICS
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Abin da ya Kamata ku Sani Kan ƙungiyar da Putin ke Karɓar Baƙuncinta: BRICS
International News

Abin da ya Kamata ku Sani Kan ƙungiyar da Putin ke Karɓar Baƙuncinta: BRICS

Attajdid
Last updated: 2024/10/25 at 3:18 AM
Attajdid Published October 25, 2024
Share
SHARE

Shugabannin ƙasashen duniya 24 sun hallara a ƙasar Rasha a ranar Talata don buɗe taron kwanaki uku na ƙungiyar BRICS, na kawancen ƙasashe masu tasowa da ke fatan ganin Kremlin za ta kalubalanci “mulkin Ƙasashen Yamma”.

 

Mecece BRICS?

Ƙasashen Brazil da Rasha da Indiya da kuma China ne suka kafa ƙungiyar ta raya tattalin arziki a shekarar 2009 inda a hukumance suka yi maraba da Afirka ta Kudu cikin ƙungiyar a sherakar 2009, kana suka faɗaɗa sunanta zuwa BRICS wanda ke nuna harafin farko na sunayen ƙasashen biyar.

 

BRICS dai ta kuɗuri aniyyar kalubalantar karfin ikon Amurka da wasu Ƙasashen Yamma a duniya.

 

Cikin sauri ta faɗaɗa bayan Iran, da Masar da Habasha da Hadadiyyar Daular Larabawa suka shiga cikin watan Janairu. Kazalika Turkiya da Azerbaijan da Malaysia da sun gabatar da takardar neman shiga.

 

BRICS tana da burin faɗaɗa muryar manyan ƙasashen masu tasowa don ƙalubalantar tsarin duniya da ƙasashen yamma ke jagoranta. Mambobin da suka kafa ta sun yi kira kan a samar da tsarin adalci a duniya da kuma gyara cibiyoyin ƙasa da ƙasa kamar Majalisar Dinkin Duniya, da Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) da Bankin Duniya.

 

Tare da ƙarin sabbin mambobi huɗu a wannan shekara, a yanzu ƙungiyar za ta kunshi kasashe tara kenan, wadanda ke kara taka rawa a tattalin arzikin duniya.

 

Ƙasahshen ƙungiyar BRICS sun ƙunshi kashi 30 cikin 100 na faɗin ƙasa a duniya, da kuma kashi 45 cikin 100 na yawan al’ummar duniya sannan da kashi 45 na yawan arzikin man fetur da ake hakowa a duniya.

 

A tare, suna sauƙaƙe kusan kashi ɗaya bisa huɗu na kasuwancin duniya.

 

Wasu muhimman batutuwa ne taron na Rasha zai fi mayar da hankali a kai?

 

Manyan batutuwan da ke cikin ajandar sun haɗa da matsayar Shugaban Rasha Vladmir Putin na tsarin biyan kuɗi da kungiyar BRICS ke jagoranta ga abokiyar hamayyarta SWIFT, cibiyar hada-hadar kuɗi ta ƙasa da ƙasa da aka cire bankunan Rasha daga ciki a shekarar 2022, da kuma tashe-tashen hankula da suka mamaye yankin gabas ta tsakiya.

 

Rasha dai ta bayyana taron a matsayin gagarumin mataki na diflomasiyya da zaitaimaka mata kulla kawance don kalubalantar “mulkin kasashen yamma”.

 

Gabanin taron, Firaministan Indiya Narendra Modi ya yaba taron yana mai kiransa da “abokan haɗin gwiwa na musamman” tsakanin Moscow da New Delhi, ya kuma ce za a tattauna kan batutuwan da suka shafi sauyin yanayi a cikin ajanda.

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid October 25, 2024 October 25, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Jigawa NUT Gets New Executive

Attajdid Attajdid December 19, 2025
Akalla An Sami Mutane 30 Sun Mutu a Ambaliyar Ruwan data Barke a Jahar Maiduguri.
Ana Cigaba da Kaiwa Juna Hari Tsakanin Isr@’ila da Dakarun Muk’awama a Gaza
Shekaru Biyun da Aka Shafe Ana Yaƙi Mafi Muni a Duniya  ya sa Sudan ta ɗaiɗaice
WANENE MUHAMMED ALBASHIR SABON FIRA-MINISTAN SYRIA
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?