Dakarun na Al-Qassam Brigades sun kai hari da makami mai linzami kirar D9 a kusa da wurin shakatawa na tashar da ke gabashin unguwar Al-Tuffah da ke gabashin birnin Gaza.
Wani jirgin saman Isra’ila ya harbi wani jariri dan watanni 6 a birnin Gaza. A wani rahoto da aka fitar yana cewa duk sa’a daya sai an sami mutuwar akalla mutum daya sabo da matsananciyar yunwa da ake fama da ita a Gaza.
Wani yaro da ke fama da matsananciyar yunwa ya je neman abinci don kansa da ‘yan uwasa, amma ya dawo da rauni sakamakon harsashin da sojojin Isra’ila suka harbeshi da shi a Gaza.
Jiragen saman Isra’ila sun kai hari kan wani tantin ‘ yan gudun hijira a Khan Yunis, kudancin zirin Gaza. An tsinto gawarwakin yaran, sun kone gaba daya.
A wani harin da sojojin Isra’ila suka kai kan wani tantin ‘yan gudun hijira a wurin Al-Tall,kudancin Deir al-Balah, Asibitin Shahidai na Al-Aqsa da Nasser ya bada tabbacin mutuwar mutane 5 tare samun wadanda suka jikkata a harin.
Mai rahoto;
M.B.S.Gama.
At-tajdid News.




