By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: SOKE YUNKURIN GYARA KUNDIN TSARIN MULKI DOMIN KARFAFA SHARI’AH DA MAJALISAR WAKILAI TA YI.
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > Books & Journal > SOKE YUNKURIN GYARA KUNDIN TSARIN MULKI DOMIN KARFAFA SHARI’AH DA MAJALISAR WAKILAI TA YI.
Books & JournalNews

SOKE YUNKURIN GYARA KUNDIN TSARIN MULKI DOMIN KARFAFA SHARI’AH DA MAJALISAR WAKILAI TA YI.

Attajdid
Last updated: 2024/11/05 at 5:34 PM
Attajdid Published November 5, 2024
Share
SHARE

Ranar 24/10/2024 rana ce ta bakin cikin ga kasar nan. Rana ce da ta nuna cewar shekaru ashirin da biyar da aka yi na demokoradiyya ba su iya samar da hakuri da juna da kasar nan ta ke bukata ba game da bambancin addini, wanda zai samar mata da zama lafiya mai dorewa.

 

A wannan rana ce aka yi waje da kudurin da Hon. Aliyu Misau, dan majalisar PDP mai wakiltar mazabar Misau/Dambam da ke Jihar Bauchi a Majalisar Wakilai ta kasa ya gabatar. Kudurin ya bukaci ne a yi kwaskwarima ga gyararren kundin tsarin mulki na 1999, domin a fadada hurumin kotunan daukaka kara na Shari’ar musulunci a matakin kasa da jihohi.

 

Kudurin ya bukaci a yi gyara ga sassa na 24, 262, 277 da 288 na tsarin mulkin domin a cire kalmar “personal”, daga jumlar da ke cewa “Islamic Personal Law”, duk inda aka kawo ta a cikin kundin tsarin mulkin.

 

Ma’ana shi tsarin mulkin ya bayar da dama ne kawai a yi wa musulmi hukunci da Shari’ar musulunci a abubuwan da suka shafi al’amurran zamantakewa da iyali, watau aure da hakkokin miji da mata da reno da saki da rabon gado. Wadannan su ake kira “Islamic Personal Law”.

 

Kudurin Hon. Aliyu Misau ya na kira da a ce “Islamic Law” kawai, a cire “Personal”. Idan aka yi haka zai zama kenan kotun Garandakadi tana da damar sauraren karar da aka daukaka zuwa gareta wadda ta shafi kowace matsala ta musulmi idan dai ba ta laifi ba ce (criminal case), ta yi hukunci na musulunci, a madadin a ce sai dai High Court kawai ke da wannan hurumin.

 

Ho. Aliyu Misau ya kawo misali cewar irin bankin Ja’iz da bankin Taj da ke kokarin bin tsarin kasuwanci na musulunci suna bukatar su kai karar rikice – rikicensu ga kotun Shari’ar musulunci. Amma idan akwai wannan kalmar “personal” ba za su iya ba.

 

Abinda lura a nan shine: duk inda aka yi maganar Shari’ar musulunci a cikin dokokin kasar nan ana magana ne a kan musulmi kawai. Ba a taba kokarin yin wata doka ba da ta yi yunkurin dankara Shari’ar musulunci a kan wanda ba musulmi ba. Rashin yin aiki da cikakkar Shari’ar musulunci a kasar nan tauyewa ne ga hakkin mu musulmi na yin Addinin mu. Babu lokacin da yi wa musulmi Shari’ar musulunci za ta cutar da wadanda ba musulmi ba, ko ta jawo ma kasa wata illa.

 

Amma dai a hakan wani gungu na kiristoci, karkashin jagorancin wani da ya yi ridda daga musulunci ya koma kirista, wai shi Bamidele Salam suka nace sai da aka yi watsi da wannan kuduri karkashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar wanda shi ma kirista ne mai suna Beni Kalu ta hayar kawai cewa “e” da “a’a”. Babu yadda za a dubi wannan aiki in ban da a ce kiyayyaya ce ta addini da tsaurin ra’ayi da rashin kulawa da bukatun abokan zama.

 

To amma ya kamata mu yi tambaya a nan. Musulmi sun fi kirista yawa ko da da kadan ne a Majalisar Wakilai. To duk ina wadannan musulmin lokacin da aka yi wannan ta’asar? Ina shugaban majalisar wanda shi musulmi ne?

 

Wannan ya sa ni na ke da ra’ayin cewa ba ma kirista ne suka yi mana yankan kauna ba, musulmi ne ‘yan uwanmu, wakilan mu, suka yi mana, ko dai saboda sun tafi harkokin gaban kansu sun ki halartar zaman majalisa har aka fi su yawa, ko kuma su ma sun goya baya ne a yi watsi da wannan kuduri.

 

Modibbon Gusau.

5/11/2024

You Might Also Like

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

UNICEF Urges Media to Advocate for Increased Water, Sanitation, and Hygiene Budget.

Attajdid November 5, 2024 November 5, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

An Kashe Jagoran ’Yan Bindigar Kaduna a Rikicin ’Yan Fashin Daji

Attajdid Attajdid September 23, 2024
Firayim Ministan Spain, Pedro Sánchez, ya bayyana cewa ƙasarsa ba za ta ci gaba da hulɗa da Isra’ila ba saboda yadda take ci gaba da kisan al’ummar Falasdinu a Gaza.
Zulum zai saya wa sojoji da ’yan sa-kai ƙarin motoci don yaƙar Boko Haram
DICON @60: MATAWALLE HAS ANNOUNCED THE UPCOMING CELEBRATION OF THE DEFENCE INDUSTRIES CORPORATION OF NIGERIA (DICON) 60th ANNIVERSARY.
Ghana ta kama baƙin haure 2,000 a ƙoƙarinta na yaƙi da bara a ƙasar
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?