SIYASAR KASASHEN WAJE A CIKIN SURIYAH LOKACIN YAKIN BASASA.
Mun yi bayanin kungiyoyin da suka bayyana a 2011 domin kokarin canja gwamnatin Basshar Assad, abinda ya haifar da yakin basasa a kasar. Yau in sha Allahu zamu ga rawar da kasashen waje suka taka a cikin wannan yakin. Kasashen da za mu yi nazari in sha Allahu su ne: Iran, Rasha, Amerika da kasashen yamma, sai kuma Turkiya da kasashen Larabawa.
1 . IRAN: Kamar yadda muka fadi a baya an samu dangantaka mai karfi tsakanin gwamnatin Suriyah da kasar Iran tun lokacin mulkin Hafiz Assad har zuwa dan shi Basshar. Babbar abokiyar fadan Iran ita ce Amerika. Wannan ya jawo rashin jittuwa tsakaninta da abokan Amerika a Gabas ta tsakiya, watau Isra’ila da kasashen Larabawa. Hakan ya sa Iran ta dauki matakin hada karfin dukkan ‘yan shi’a da ke cikin kasashen Gabas ta tsakiya saboda su zama masu taimaka wa manufofinta, su kuma zama barazana ga abokan adawarta.
Kasar Suriyah tana da muhimmanci a cikin wannan tsarin na Iran. Ana kiran kasashe da kungiyoyin da Iran ta hada a cikin wannan shiri da sunan “Yankin gwagwarmaya” (Axis of Resistance), (محور المقاومة). Ma’ana suna gwagwarmaya da mamayar da Amerika ta yiwa yankin gabas ta tsakiya. Kasashen sun hada da Irak da Suriyah wadanda ke karkashin mulkin ‘yan shi’a, sai kuma bangaren Yaman da ‘yan shi’ar Huthi ke mulki. Sai kungiya daya ta shi’a, ita ce Hizbullahi ta Lebanon. Sai kuma kungiyoyin gwagwarmaya na Falasdin wadanda dukkansu ‘yan Ahlus Sunnah ne, su ne kawai ba shi’a ba a cikin wannan tsarin na Iran.
Saboda haka duk wanda ya yi barazana ga gwamnatin Basshar Assad kasar Iran kai tsaye za ta yi iyakar karfinta don ba shi kariya. Haka kuwa ya faru a wannan yakin na Suriyah. Kai tsaye kasar Iran ta shigar wa Basshar da ta ga alamun za a yi galaba a kan shi.
Kasar Iran ta taimaka wa gwamnatin Basshar a wannan yakin basasa ta hanyoyin uku:
i . Shiga kai tsaye: Iran ta dauki nauyin bai wa Basshar Assad makamai da za su taimaka mashi ga yakin, har da jirage marasa matuka (drones). Sannan ta turo sojojinta na daula na kasa da na sama, tare da dakarun ba da kariya ga juyin juya hali (Islamic Republic Revolutionary Guards Corps, IRGC) domin su yiwa Basshar yaki.
ii . Amfani da dakarun Hizbullahi na Lebanon: Iran ta ba da umurni ga Kungiyar nan ta ‘yan shi’a da ke Lebanon karkashin jagorancin Hassan Nasrallah mai suna “Hizbullahi” da su kawo wa Basshar dauki. Nan take kuwa suka turo mafi kwarewar dakarunsu da aka fi tsoro, wadanda ake kira “Bataliyar Radhwan” suka dinga fatattakar masu yiwa Basshar tawaye.
iii . Tara mayakan shi’a na kasa da kasa: Matakin na uku da Iran ta dauka domin hana kifewar gwamnatin Basshar a 2011 shine ta tattaro mayaka daga dukkan kasashen da ‘yan shi’a suke da yawa, kamar Irak da Afghanistan da Pakistan da sauransu domin su taya Basshar yakar masu yi mashi jayayya.
A takaice dai tun daga fara wannan yakin har ranar da aka samu sulhu Iran ita ce babbar wadda ta ke tallabe da gwamnatin Basshar. Ta kuma mayar da yakin kamar wani yaki tsakanin Shi’ah da Sunnah.
A darasi na gaba zamu duba rawar sauran kasashen da muka ambata in sha Allahu.
Modibbon Gusau.
13/06/1446
15/12/2024.




