By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Sunan Muhammad ya Sake Zama Kan Gaba a Sunayen da Ake Raɗawa Jarirai a England Wales
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Sunan Muhammad ya Sake Zama Kan Gaba a Sunayen da Ake Raɗawa Jarirai a England Wales
International News

Sunan Muhammad ya Sake Zama Kan Gaba a Sunayen da Ake Raɗawa Jarirai a England Wales

Attajdid
Last updated: 2025/08/01 at 1:43 PM
Attajdid Published August 1, 2025
Share
SHARE

An fitar da sunayen jarirai da suka fi tashe a shekarar 2024 a Ingila da Wales, inda Athena da Yahya suka shiga cikin guda 100 na farko da aka fi sanya wa yara a karon farko.

 

BBC ta rawaito cewa Muhammad ya zama na ɗaya a ɓangaren maza, shekara biyu ke nan a jere, inda Noah da Oliver suka zo na biyu da na uku, kamar yadda yake a shekara ta 2023.

 

Olivia da Amelia ne sunayen yara mata na ɗaya da na biyu da aka fi sanyawa, karo na uku a jere, sai dai Isla ya fita daga cikin ukun farko a sunayen da aka fi sanya wa yara mata, inda Lily ya maye gurbinsa.

Ofishin ƙididdiga na Birtaniya ne ya fitar da alƙalumar, wanda shi ne ke tattara bayanan takardar rajistar haihuwa.

 

Sabbin sunayen yara mata da suka shiga 100 na farko su ne Eloise da Nora da Myla da Rosa da Athena da Sara da kuma Zoe.

 

A ɓangaren maza kuma akwai Austin da Nathan da Vinnie da kuma Yahya.

 

Muhammad ya kare kambinsa na sunan da aka sanya wa jarirai maza ne inda aka sanya wa yara 5,721 sunan. Ya zamo sunan da aka sanya wa jarirai a yankuna biyar cikin tara na Ingila, sannan na 57 a Wales.

 

Haka nan sauran yadda ake rubuta sunan, kamar Mohammed, shi ne na 21 inda aka sa wa jarirai 1,760, sai kuma Mohammad a matsayin na 53, wanda aka sanya wa jarirai 986.

 

Mai rahoto;

Salihu Garba.

 

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid August 1, 2025 August 1, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
International News

Hamas ta sanar da kashe sojojin Isra’ila da dama da jikkata wasu

Attajdid Attajdid May 25, 2025
Isra’ila ta Kashe Mataimakin Shugaban Hukumar Kare Farar Hula ta Gaza
HADEJIA STATE: Senator Ahmad Renaissance the Struggles
Mayaƙan Boko Haram Sun Miƙa Wuya ga Sojojin Nijeriya
Zanga-zanga ta ɓarke kan zargin sojoji da kashe mata a Adamawa
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?