By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Bayan Korar Sojojin Amurka Daga Nigar  Wacce Kasa Zasu Koma Afarka.
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Bayan Korar Sojojin Amurka Daga Nigar  Wacce Kasa Zasu Koma Afarka.
News

Bayan Korar Sojojin Amurka Daga Nigar  Wacce Kasa Zasu Koma Afarka.

Attajdid
Last updated: 2024/08/26 at 3:39 PM
Attajdid Published August 26, 2024
Share
SHARE

Bayan da Nijar ta kori sojojin Amurka daga ƙasar, Amurka ta ce tana kai dakarun nata wasu ƙasashe ƙawayenta da ke yankin.Amurka ta sanar da cewar ba ta da wani shiri na kafa sansanin soji a Nijeriya, inda ta kuma ce tana aika sojojinta da ta janye daga Nijar zuwa ƙasashen Afirka da suke ƙawance da ita.

Manjo Janar Kenneth P. Ekman, jagoran Dakarun Amurka a Yammacin Afirka da ke ƙarƙashin AFRICOM ne ya bayyana hakan a yayin ganawa da ‘yan jarida a ƙarshen mako a Abuja.

Bayan amincewa da janye dakarunta daga Nijar baki ɗaya a farkon shekarar nan saboda taɓarɓarewar alaƙar diflomasiyya da gwamnatin sojin ƙasar ta yankin Sahel, an samu wasu rahotanni da ke cewa Amurka za ta mayar da sansaninta zuwa Nijeriya.

Tuni gwamnatin Nijeriya ta musanta wannan zargi, wanda Manjo Ekman ya tabbatar da hakan a yanzu.”Ina son shaida muku cewa babu wasu shirye-shirye na kafa sansanin sojin Amurka a Nijeriya, kuma na so na zanta da ku ne saboda batun na da muhimmanci,” in ji Ekman.

Ya ce “Na fahimci yadda wanzuwar sojojin Amurka ke zuwa da amfani da kashe kuɗaɗe, duba ga yanayin da ake ciki, kuma ina son tabbatar muku cewa ba wannan batun ne ya kawo ni nan ba, babu wannan shiri.

Abin da na zo tattaunawa shi ne batun tsaron yankin wanda yake shafar Nijeriya.”Jami’in sojin na Amurka ya ƙara da cewar ya zo Nijeriya ne don jin ra’ayin shugabannin soji da na fararen-hula a ƙasar kan ayyukan Amurka na samar da tsaro a yankin.

Ana buƙatar sauraro, kuma wannan ce gaɓar, wannan ne babban dalilin zuwan. Na fahimci yadda kasancewa ta a nan ke da amfani, ƙari kan ziyarar sauran shugabannin Amurka. Mataimakiyar Minista Stewart ta zo nan kwanakin baya, inda ta tattauna kan Ma’aikatar Tsaron Amurka da DOD nexus, inda ta taɓo alhakin da ake da shi na amfani da ƙirƙirarriyar basira wajen ayyukan soji,” in ji Ekman.

Ya ci gaba da cewa daga batutuwan da suka tattauna da mahukuntan Nijeriya sun haɗa neman mafita ga matsalolin tsaron da ke damun ƙasar, da yadda taimakon tsaro daga Amurka zai kawo sauyi.

Manjo Janar Ekman ya kuma ƙara da cewar tuni aka fara kai sojojin Amurka da aka janye daga Nijar zuwa ƙasashen Afirka da ke makotaka da Nijar, musamman ma Cote d’Ivoire da Benin.

At-tajdid News.

You Might Also Like

Speakers Forum Congratulates Kwara, Katsina Speakers for Securing Governorship, Senate Tickets

Jigawa Governor: Our One Million Votes for Tinubu Are Non-Negotiable , Irreversible

Governor Namadi Affirmed as APC Jigawa State Gubernatorial Candidate for 2027

APC Primaries: Jigawa Speaker Retains Ticket Unopposed

Nursing Mother Inmate Freed as Jigawa NLC Women’s Wing Clears Her Court Fines

Attajdid August 26, 2024 August 26, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
International News

Sojojin Isra’ila 130 Sun Sanya Hannun Dakatar da Yakin da Suke yi a Gaza 

Attajdid Attajdid October 16, 2024
FARKAWA DAGA BARCI: ƳAN AUSTRALIA SUN SHIGA YUNKURIN YAJIN YUNWA DON FALLASA KISAN KIYASHI A GAZA DA CIKIN GIDANSA 
MENENE AIKIN KUNGIYAR (HAMAS)????
Babban sufetan Yan sandar kasar nan Yace aikata miyagun laifuka na raguwa Sosae a Nigeria…..
An Yi Jana’izar Baturkiyya-Ba’amurkiya ‘Yar Gwagwarmaya Da Aka Kashe a Gabar Yammacin Kogin Jodan
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?