By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Sojojin Isra’ila 130 Sun Sanya Hannun Dakatar da Yakin da Suke yi a Gaza 
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Sojojin Isra’ila 130 Sun Sanya Hannun Dakatar da Yakin da Suke yi a Gaza 
International News

Sojojin Isra’ila 130 Sun Sanya Hannun Dakatar da Yakin da Suke yi a Gaza 

Attajdid
Last updated: 2024/10/16 at 8:50 PM
Attajdid Published October 16, 2024
Share
SHARE

 

Rundunar sojin Isra’ila ta fara dakatar da jami’anta da dama da suka ce za su daina aikin soji da yaƙi a Gaza har sai gwamnati ta amince da yarjejeniyar musayar fursunoni don dawo da Isra’ilawar da aka yi garkuwa da su gida.

 

“Dakatar da sojojin, ciki har da manya biyar da ke matsayin jiran ko-ta-kwana, ta fara ne a ‘yan kwanakin nan ta hanyar kiran waya ga dukkan waɗanda suka sanya hannu a madadinsu – ciki har da kiran da aka yi wa sojan da ke aiki a Gaza,” in ji jaridar Haaretz a ranar Talata.

 

“Ɗaya daga cikin waɗanda suka sanya hannun ya faɗa wa wani soja cewa manyansa sun nemi ya sanya hannu a wasiƙar, amma ya ƙi yin hakan,” in ji jaridar.

Wani soja kuma ya bayyana kiran wayar da ‘barazana’, inda wani kuma ya ce kwamandan bataliyarsu ne ya yi kiran waya mai tsayi, wanda hakan ya janyo aka dakatar da shi, in ji jaridar.

 

Mummunar tattaunawar Netanyahu;

Rahoton na Haaretz ya ƙara da cewa a makon jiya ne sojoji 130 suka sanya hannu kan wata wasiƙa inda suka sha alwashin ba za su ci gaba da aikin soji ba har sai gwamnati ta amince da tsagaita wuta a Gaza tare da tabbatar da an yi musayar fursunonin da ke tsare.

 

An rubuta wasiƙar ga Firaminista Netanyahu, ministoci, da shugaban rundunar soji Herzi Halevi.

 

Isra’ila ta yi ƙiyasin akwai mutanenta 101 da ake tsare da su a Gaza, inda Hamas kuma ta ce an kashe mutanen a hare-haren kan mai-uwa-da-wabi da Isra’ila ta kai yankin.

 

Yunƙurin shiga tsakanin da Amurka, Masar da Qatar ke yi don tsagaita wuta a Gaza da musayar fursunoni tsakanin Isra’ila da Hamas ya ci tura saboda Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya ƙi dakatar da yaƙi inda yake ci gaba da kawo sabbin sharuɗɗa.

 

Sharuɗɗan sun haɗa da karɓe iko da Hanyar Philadelphi da ke tsakanin Gaza da Masar, fita ta ƙofar Refay da hana mayaƙan Falasɗinawa dawowa arewacin Gaza ta hanyar tantance masu dawowa ta hanyar Netzarim.

 

Hamas ta nace cewa lallai Isra’ila ta janye gaba ɗaya daga yankin kafin ta amince da wata yarjejeniya.

 

Ci gaba da kisan kiyashi;

Tun bayan harin 7 ga Oktoban 2023 Isra’ila ta fara kai hare-hare Gaza tana aikata kisan kiyashi, duk da kiran tsagaita wuta da Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi.

 

Ta kashe fiye da mutane 42,300, galibinsu mata da yara, kana ta jikkata fiye da 99,000 a yaƙin.

 

Hare-Haren Isra’ila ya raba kusan dukkan jama’ar Gaza da matsugunansu a yayin da ƙawanyar da aka yi musu ta janyo ƙarancin abinci, ruwan sha mai tsafta, da magunguna.

 

Isra’ila na fuskantar tuhumar aikata kisan kiyashi a Kotun Ƙasa da Ƙasa.

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid October 16, 2024 October 16, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sauke Shugabannin Riƙo na Kananan Hukumomin Jihar 44

Attajdid Attajdid September 19, 2024
Ana Saran Za a Cimma Mastaya Akan Tsagaita Da Kuma Musayan Bursunonin Falasdinu da Isra’ila.
Double Tragedy: – Jigawa Governor Loses elder Son Again
Propcom, NBA Condole Jigawa Governor Over His Mother, Son Death 
Auto crash kills 21 Kano Athletics, Govt Declared Monday Public Holiday 
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?