A wani babban mataki na tarihi, babbar kotun jihar New South Wales (NSW) ta amince da gudanar da zanga-zangar “March for Humanity” a kan Harbour Bridge da ke Sydney, ya kasar Australia duk da matsin lamba daga gwamnati da ƙungiyoyin goyon bayan Isra’ila.
An shigar da ƙara domin dakatar da gangamin, amma kotun ta watsar da ƙarar, tana mai bai wa masu zanga-zanga dama su gudanar da taron kamar yadda aka tsara a ranar Lahadi mai zuwa.
> Ana sa ran taron zai ja dubban mutane fiye da 100,000, domin jaddada bukatar dakatar da kisan kiyashi da ake yi a Gaza da kuma nuna damuwa da halin da al’ummar Falasɗinu ke ciki.
RAHOTO DAGA: Yaya Babba
AT-TAJDID NEWS




