By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Akwai Barazanar Yaduwar Cutar Faran kamar Biri ( Mpox) a Nigeria.
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Akwai Barazanar Yaduwar Cutar Faran kamar Biri ( Mpox) a Nigeria.
News

Akwai Barazanar Yaduwar Cutar Faran kamar Biri ( Mpox) a Nigeria.

Attajdid
Last updated: 2024/08/31 at 10:38 AM
Attajdid Published August 31, 2024
Share
SHARE

Kamar Yadda NCNC ta Bayyana Kawo Yanzu ba a Samu Wanda ya Mutu baHukumar Yaƙi da Cutuka Masu Yaɗuwa a Nijeriya (NCDC) ta ce an samu ƙaruwar mutanen da suka kamu da cutar farankamar biri wato mpox a jihohi 20 da kuma Babban Birnin Tarayya, inda yanzu adadin waɗanda suka kamu da cutar ya kai 48.

NCDC ta bayyana haka ne a saƙon da ta fitar a shafukanta na sada zumunta ranar Juma’a.

Hukumar ta ce a mako ɗaya daga ranar 19 zuwa 25 ga watan Agusta kaɗai mutum takwas ne suka kamu da cutar, inda aka samu masu cutar guda huɗu a jihar Enugu, sai ɗai-ɗai a jihohin Bayelsa, Cross River, Edo da Osun.Nijeriya ta ƙara sanya ido a duk hanyoyin shiga ƙasar don hana yaɗuwar cutar Farankamar Biri Ta ƙara da cewa cutar ta fi shafar yara daga shekara ɗaya zuwa shekara biyar.

NCDC ta bayar da sanarwar ce a yayin da ƙasar ta karɓi allurai 10,000 na rigakafin farankamar biri daga Amurka ranar 27 ga watan Agusta.

Tuni dai Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta ayyana cutar a matsayin wani lamari da ke buƙatar ɗaukin gaggawa a yayin da take ci gaba da yaɗuwa a kasashin Afirka.

MAICECE CUTAR (Mpox) KUMA TAYA AKE KARE KAI DAGA KAMUWA DA ITA ? Mece ce mpox?Mpox cuta ce da ake ɗauka daga ƙwayar cutar bairos. Kuma alamunta su ne zazzaɓi, da ciwon kai da ciwon baya da ciwon gaɓoɓi da kasala da yawan gajiya da kumburi.

Ƙuraje za su iya fesowa su kuma watsu a gaba ɗayan jiki, sai dai sunfi yawa a fuska, sannan daga baya su bushe su riƙa ɓarewa daga jiki.

Ƙwayar cutar mpox na janyo rashin lafiya a mafi yawan lokuta. Alamunta za su iya bayyana tsakanin kwana biyar zuwa 21 bayan kamuwa.Ya take yaɗuwa?Ƙwayar cutar za ta iya yaɗuwa idan mutum ya taɓa mai ɗauke da cutar ko ya taɓa wani abin da mai cutar ya taɓa ya kuma gurɓata shi.Sai dai haɗarin yaɗa cutar ga jama’a ba shi da yawa.

Ƙwayar cutar ta fi kama yara kuma zuwa kaso goma cikin ɗari na waɗanda suka kamu da mpox za su iya mutuwa.A ina ake samun mpox?Cutar Mpox ta samo asali ne daga dazuzzuka a ƙasashe masu zafi a Tsakiya da Yammacin Afirka kuma tana yaɗuwa tsakanin dabbobin daji.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce har yanzu ba a gano ‘ainihin inda mpox take tasowa ba’ sai dai ƙwayar cutar ta fi yaɗuwa ne a tsakanin ɓeraye da birrai.A ina aka fara gano mpox? An fara gano cutar a 1958 bayan cuta mai kama da ƙyanda ta ɓarke a cikin birai da aka yi amfani da su wajen bincike.An fara gano cutar a jikin mutane a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo a 1970

A ranar 13 ga Agusta, Cibiyar Yaƙi da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta bayyana cutar a matsayin annoba a duka faɗin nahiyar.

A lokacin da ƙwayar cutar ta mpox nau’in clab 1b mai haɗari da saurin yaɗuwa a baya ta yaɗu daga Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo zuwa iyakokin ƙasashe maƙota kamar Burundi da Kenya da Rwanda Uganda.

Shin akwai maganin cutar?A yanzu dai babu wani takamaiman maganin mpox.

Akwai riga-kafi uku da ake da su da kuma a Janairun 2022 Hukumar Magunguna ta Turai ta amince a yi amfani da wani magani da aka samar na cutar agana don jinyar mpox, sai dai bai wadata ba a cikin jama’a.

Hukumar Yaƙi da Cutuka Masu Yaɗuwa ta Nijeriya (NCDC) ta ce akwai matakan da za a iya ɗauka a matsayin riga-kafin cutar, waɗanda suka haɗa da Nisantar duk dabbodin da ke iya yaɗa cutar da suka haɗa da marasa lafiya da mushe a wuraren da aka samu mpox da nisantar duk wani abu da dabbar da ba ta da lafiya ta taɓa Killace dabbobin da aka ga alamun sun kamu da cutar, kada su haɗu da sauran dabbobi.Dafa naman dabbobi da ƙwansu da nononsu sosai kafin a ci ko a sha.

Keɓe mutanen da suka kamu, da kuma saka kayan kariya duk lokacin da za a je wajensu. Wanke hannu a-kai-a-kai bayan kula ko ziyartar marasa lafiya. Wayar da kan mutane kan cutar da matakan kariya.

At-tajdid News.

You Might Also Like

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

UNICEF Urges Media to Advocate for Increased Water, Sanitation, and Hygiene Budget.

Attajdid August 31, 2024 August 31, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Civil Society Lauds Distribution Of 3.7 Million Mosquito Nets In Jigawa

Attajdid Attajdid August 19, 2024
KANO PENSIONER DONATES GRATUITY FOR MOSQUE PROJECT 
DA ƊUMI-ƊUMI: Shugaban Kasar Burkina Faso Ibrahim Traore Ya saka dokar biyan tarar miliyan biyu da zaman gidan yari Na dindindin ga duk macen da ta bayyana tsiraicinta a kafafen sadarwa na zamani.
Gaza anti-war protesters clash with police at Australian arms fair as police deploy tear gas and stun grenades to disperse crowd flinging horse manure and setting bins alight.
Zulum Names Housing Estate after VP Shettima
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?