By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: BURKINA FASO, NIJAR DA MALI SUN KAI KARAR KASAR UKRAINE  GABAN  MDD  AKAN ZARGIN TA’ADDANCI
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > BURKINA FASO, NIJAR DA MALI SUN KAI KARAR KASAR UKRAINE  GABAN  MDD  AKAN ZARGIN TA’ADDANCI
International News

BURKINA FASO, NIJAR DA MALI SUN KAI KARAR KASAR UKRAINE  GABAN  MDD  AKAN ZARGIN TA’ADDANCI

Attajdid
Last updated: 2024/08/21 at 7:45 AM
Attajdid Published August 21, 2024
Share
SHARE

Ƙasashen uku suna so Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ɗauki  ”matakan da suka dace” a kan Ukraine, suna masu cewa tana ”ƙarfafa gwiwar ƙungiyoyin ta’addanci a Afirka.

”Ƙasashen uku suna so Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ɗauki  ”matakan da suka dace” a kan Ukraine, suna masu cewa tana ”ƙarfafa gwiwar ƙungiyoyin ta’addanci a Afirka.

Burkina Faso, Mali da Jamhuriyar Nijar sun kai ƙarar Ukraine a gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ranar Talata inda suka zargi gwamnatin ƙasar da fitowa “fili tana goyon bayan ƙungiyoyin ‘yan ta’adda na duniya” musamman a yankin Sahel.

Ƙasashen uku sun ɗauki matakin ne bayan wasu kalamai da jami’an diflomasiyyar Ukraine suka yi a kwanakin baya da ke nuna rawar da ƙasarsu ta taka a hare-haren da Abzinawa ‘yan tawaye suka kai wa sojojin Mali a watan jiya a yankin Tinzawaten na kan iyaka da Algeria inda suka kashe sojoji da dama.Wannan batu dai ya sa Mali da Nijar sanar da yanke duk wata hulɗar jakadanci da Ukraine.Mali ta yanke hulɗa da Ukraine kan zargin goyon bayan ‘yan ta’adda.

A wata wasiƙa da ministocin ƙasashen uku suka aike wa Kwamitin Tsaro na MDD, sun bayyana matuƙar kaɗuwarsu bisa kalaman da mai magana da yawun rundunar leƙen asirin Ukraine Andriy Yusov, ya yi cewa, “na amincewa da rawar da Ukraine ta taka a hare-haren dabbanci kuma na matsorata da masu aikata lafuka suka kai wa” dakarun Mali daga ranar 24 zuwa 26 ga watan Yuli.

Wasiƙar ta ƙara da cewa jakadancin Ukraine a Senegal Yurii Pyvovarov shi ma ya tabbatar da rawar da ƙasarsa ta taka wurin kai wa sojojin Mali hari.

Yusov ya ce ‘yan tawayen sun samun “dukkan bayanan da suke buƙata” domin kai hari kan sojojin Mali da abokansu sojojin haya na Wagner na ƙasar Rasha. Sojojin na Wagner na cikin waɗanda ‘yan tawayen suka kashe, a cewar hukumomi.

Ƙasashen uku sun yi kira ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya ɗauki ”matakan da suka dace” a kan Ukraine, saboda matakin da ta ɗauka na ”ƙarfafa gwiwar ƙungiyoyin ta’addanci a Afirka.

””Waɗannan ayyuka sun keta ‘yancinmu na kasancewa ƙasashe masu cin gashin kawunansu, kuma ya nuna ƙarara yadda aka yi kutse tare da goyon bayan ƙungiyoyin ta’addanci na duniya, lamarin da ya saɓa wa Yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran dokokin ƙasashen duniya,” in ji wasiƙar.

(TRT AFRIKA)

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid August 21, 2024 August 21, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Za mu kare masu zanga-zangar tsadar rayuwa matuƙar ta lumana ce – ‘Yan Sandan Najeriya.

Attajdid Attajdid July 25, 2024
TARIHIN SHUGABAN OFISHIN SIYASA NA HARKAR HAMAS, JAGORAN MUJAHID YAHYA AL-SINWAR “Abu Ibrahim”
NAGGW Solicits Jigawa’s Support to Combat Environmental Degradation 
Sakon zuwa ga Daliban Sheikh Bashir Nuhu Assalafy kashi na (36)
Duniya ba za ta iya jiran amincewar Isra’ila don aiwatar da yarjejeniyar samar da ƙasa biyu ba a yankin kasar Palastinu — Fidan
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?