DAKARUN ISRA’ILA SUNA CI GABA DA MAMAYAR WURAREN PALESDINAWA.
Dakarun mamaya na Isra’ila sun mamaye sansanin Al-Ain da ke birnin Nablus a gabar yammacin kogin Jordan kuma sun kama wasu matasa biyu a sansanin.
A cigaba da mamaya sun mamaye birnin Qalqilya da ke gabar yammacin gabar kogin Jordan tare da kewaye wani gini na zama.
A wata majiyar cikin gida: An gano gawar shahidi Iyad a-Najjar mai bukata ta musamman bayan da sojojin mamaya suka yi masa kisan gilla a gidansa da ke gabashin birnin Khan Yunus a kudancin zirin Gaza.
Ministan Ilimi na Falasdinu Amjad Barham: ya bayyana cewa “dalibai 10,000 da malamai 400 ne suka yi shahada a harin da Isra’ila ta kai a Zirin Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata a yakin Gaza”.
Hamas ta fitar da bayani akan mummunan keta haddin da aka yi a sansanin Sde Teman ya tabbatar da yanayin mamayar keta darajar ɗan adam.Ta kuma kara da cewa sharuɗɗan Netanyahu sun haɗa da ja da baya daga abin da masu shiga tsakani suka ruwaito a matsayar Isra’ila akan Gaza.
A wani labaran kuma Netanyahu ya bayyana “Hezbollah tare da goyon bayan Iran, sun harba makami mai linzami na Iran a Majdal Shams, kuma kasar Isra’ila ba za ta zura ido ba.”
Mai rahoto;
Musa Badamasi Gama.
At-tajdid News.




