Hezbollah ta tabbatar da kisan shugabanta Hassan Nasralla
Kungiyar Gwagwarmaya ta Hozbullah ta tabbatar da mutuwar shugabanta Shiekh Hassan Nasrallah sakamakon wani harrin yaaddanci da kasar Isra’ila ta kai a Buirut ta kasar Labanan.
Tun da farko shugaban rundunar
sojojin Isra’ila Laftanar Kanar Nadav Shoshani ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa sun hallaka HassanNasrullah a wani mummunan hari da suka kai.
Ikirarin da Isra’ila ta yi na kashe Hassan Nasrallah, matakin da ake kallo a matsayin babban koma-baya ga ƙungiyar Hezbollah da ke ƙasar Lebanon wadda ya jagoranta tun shekarar 1992.
“Ba a ji ɗuriyar Sayyed Hassan Nasrallah ba tun ranar Juma’a da maraice,” a cewar majiyar, wadda ta buƙaci a ɓoye sunanta saboda girman lamarin.
Nasrallah shi ne mutum mafi ƙarfin faɗa a ji da Isra’ila ta kashe a makonnin da ta kwashe tana kai hare-hare kan mayaƙan Hezbollah.
Isra’ila ta ƙaddamar da jerin zafafan hare-hare a kudancin Beirut ranar Juma’a da daddare wanda shi ne mafi girma da ta kai a yankin da Hezbollah ta fi ƙarfi tun yaƙin da suka yi a shekarar 2006.
Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta Lebanon ta ce mutane shida sun mutu sannan mutum 91 sun jikkata a hare-haren na ranar Juma’a, waɗanda suka ruguza rukunan gidaje shida.
Mai rahoto
Mustapha Garba Usman




