Red Cross ta ce ta kwashe jami’an tsaron DR Kongo fiye da 300 daga Goma
Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta ce ta kwashe sojojin gwamnatin Kongo da ƴansanda fiye da 300 daga birnin Goma da ke gabashin ƙasar cikin tsawon mako biyu.
Birnin Goma ya faɗa hannun ƙungiyar ‘yan tawayen ta M23 da ke samun goyon bayan Rwanda a watan Janairu bayan wani ƙazamin faɗa.
Majiyoyin Majalisar Dinkin Duniya sun ce kusan sojoji da ƴansanda dubu biyu ne suka nemi mafaka a sansanonin dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD.
Mai Rahoto
Mujahid Muhammad Tasiu
AT-TAJDID NEWS




