Gwamnatin jihar Kebbi, ta amince da biyan Naira dubu saba’in da biyar a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan jihar.
Da yake jawabi jim kadan bayan sanya hannu kan dokar, Gwamna Nasir Idris, ya bayyana cewa bayan karbar rahoton kwamitin hadin gwiwa na kungiyar kwadago da gwamnati tare da shawarwari guda uku, gwamnatin ta amince da zabi na biyu na Naira dubu 75 a matsayin sabon mafi karancin albashi.
Gwamnan, ya ce za a bada mafi karancin albashin ne a dukkan bangarorin ma’aikatan gwamnati da na kananan hukumomi.
Ya umarci ma’aikatar kudi ta jihar da ta fara biyan sabon mafi karancin albashin nan da kwanaki uku.
Shugaban kungiyar kwadago ta kasa NLC, Kwamared Joe Ajaero da majalisar zartarwarsa sun halarci wajen rattaba hannu kan mafi karancin albashin ma’aikatan a dakin taro na gidan gwamnati dake Birnin Kebbi.
Radio Nigeria Kaduna.
At-tajdid News.




