Gaza, 28 Yuli 2025 —
Bayan sanarwar Zionist Israel ta cewa za ta yi saurin shigar da motocin agaji tare da rungumar zaman lafiya na dan lokaci, rahotanni daga cikin Gaza sun tona asirin makirci da yaudara da Isra’ila ke yi don kawata kanta a idon duniya.
1. “Truce” Da Kisan Kare Dangi Na Ci Gaba
Isra’ila ta fitar da sanarwar tsagaita wuta don agaji, wadda ta bazu a duniya gaba ɗaya. Amma kisan kare dangi ya ci gaba da gudana, inda zuwa rana tsaka aka rigaya aka samu shahadar sama da mutane 60 a ranar farko.
2. Motoci 70 ne kawai suka shiga — kuma an sace yawancinsu
Duk da rahotannin da ke cewa “daruruwan motoci” sun shiga Gaza, gaskiya ba su haura 70 ba. Yawancin motocin agajin an sace su kafin su isa dakunan ajiya, yayin da Tel Aviv ta fi damuwa da yin hoton su wucewa domin yaudarar kafafen watsa labarai.
3. Isra’ila ta nufi tallata hoton agaji ba isar da shi ba
An tilasta motocin su bi hanyoyi masu hadari, wanda dama Isra’ila ta san za a sace su, kuma jiragen yaki na sintiri sun hallaka matasa da ke ƙoƙarin kare motocin. Babban burinsu shi ne duniya ta ga hoton agaji — ba su damu da ya isa ga yunwa-sha ba.
4. Sauke Agaji daga Jiragen Emirates: Wulakanci Ne Cikakke
Jiragen Emirates sun sauke kayan agaji a Gaza, amma abinda aka sauke bai kai kayan da motoci uku ke ɗauka ba. Wannan ya zama wasan kwaikwayo na ji-ta-kayi da tallan rahama, wanda Tel Aviv ke son duniya ta karɓa.
5. Mutuwa Daga Yunwa Na Karuwa Cikin Sauri
Yayin da wasu kafofin watsa labarai ke cewa mutuwar na faruwa ne daga “malnutrition”, gaskiya ita ce: yara da tsofaffi na mutuwa kai tsaye daga yunwa.
6. Dokoki Sun Nuna: Ko An Shigo da Madara, Jikin Yara Da Yawa Bazai Iya Jurewa Ba
Likitoci da dama a Gaza sun bayyana cewa jikin wasu jarirai da yara sun lalace matuka, har ko da aka samu abinci, bazai iya farko ko daukar magani ba.
7. Makirci Na Ƙarya Don Karkatar da Hankali
Abin da ya faru a wannan rana ta farko shi ne makircin yada ƙarya a duniya, inda Isra’ila ta shirya jan hankalin duniya ta kafar labarai, tana cewa an warware yunwa da buɗe iyaka — alhali iyakar ba a taɓa buɗewa ba, kuma agaji bai isa wanda ke bukata ba.
Kammalawa: Gaza tana ci gaba da zubar da jini da hawaye, yayin da duniya ke kallon hotunan ƙarya. Wannan al’amari ya nuna cewa yak’i ba kawai da makami ake yi ba — amma da ƙarya da labaran yaudara.
Rahoto daga: Amb. Mujahid | Tushen Bayani: Ali Abo Rezeq
At-Tajdid News




