Rasha ta hallaka mutum 12 a wani sabon hari a Ukraine
Aƙalla mutum 12 ne aka kashe sannan gommai suka jikkata a wasu jerin hare-haren jirage marasa matuka da kuma na makaman linzami da Rasha ta kai Ukraine cikin dare, a cewar jami’an ba da agaji.
An kashe wasu yara uku a birnin Zhytomyr a yammacin Kyiv, an kuma kashe wani dattijo mai shekara 70 a birnin Mykolaiv, in ji jami’an agajin gaggawa.
Harin na zuwa kwana guda bayan da babban birnin Ukraine, Kyiv ya fuskanci hare-hare masu muni wanda ba a gani ba tun soma mamayar Rasha.
Harin na ranar Asabar wanda ya hallaka mutum 13 a faɗin Ukraine, ya zo ne a daidai lokacin da ake tattaunawar diflomasiyya don ganin an kawo karshen yaƙin, ciki har da musayar fursunoni – sai dai Rasha ta bijirewa kiran tsagaita wuta.
Mai Rahoto
Mujahid Muhammad Tasiu
AT-TAJDID NEWS




