By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: An kama Hakimi kan zargin taimaka wa ’yan bindiga a Neja
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > An kama Hakimi kan zargin taimaka wa ’yan bindiga a Neja
News

An kama Hakimi kan zargin taimaka wa ’yan bindiga a Neja

Attajdid
Last updated: 2025/05/25 at 7:56 PM
Attajdid Published May 25, 2025
Share
SHARE

An kama Hakimi kan zargin taimaka wa ’yan bindiga a Neja

 

Rahotanni sun nuna cewar mutanen na taimaka wa ‘yan bindiga wajen kai hare-hare

 

 

An kama Hakimi kan zargin taimaka wa ’yan bindiga a Neja

Rahotanni sun nuna cewar mutanen na taimaka wa ‘yan bindiga wajen kai hare-hare a yankunan.

 

 

Jami’an ’yan sanda tare da haɗin gwiwar ’yan sa-kai sun kama hakimin ƙauyen Guiwa da ke Ƙaramar Hukumar Mashegu a Jihar Neja.

 

Hakimin mai suna Garba Mohammed ana zarginsa da taimaka wa ’yan bindiga wajen aikata ta’addanci a yankin.

 

Ndume ya jinjina wa Tinubu kan bai wa ’yan Arewa sabbin muƙamai

Halin da fasinjoji ke ciki bayan hatsarin jirgin sama a Ilori

An kama shi tare da wasu mutum 13 a safiyar ranar Juma’a da misalin ƙarfe 9 na safe, bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewar suna hannu wajen taikoman ’yan bindiga.

 

Rahotanni sun bayyana cewa hakimin yana bai wa ’yan bindiga mafaka a gidansa, inda suke taruwa suna shirya kai hare-haren.

 

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar wa Aminiya kama hakimin ta wayar tarho.

 

Ya ce kama mutanen na daga cikin wani samame da ’yan sanda da ’yan sa-kai ke yi domin kawar da ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a yankin Mashegu.

 

A ranar 22 ga watan Mayu, 2025, rundunar ta kai samame dazukan Magaman-Daji da kewaye, inda suka fatattaki masu aikata laifi.

 

A ranar 23 ga watan Mayu, 2025 da misalin ƙarfe 9 na safe, rundunar ta sake afkawa ƙauyukan Guiwa da Telle bisa sahihan bayanai, inda aka kama hakimin Guiwa, Mallam Garba Mohammed, bisa zargin taimaka wa ’yan bindiga.

 

An gano babura huɗu da shanu 10 a gidansa, waɗanda ake zargin na ’yan bindiga ne.

 

Sauran mutum 13 an kama su a sassa daban-daban na Mashegu bisa zargin hannunsu a ta’addanci.

 

SP Abiodun, ya ce ana gudanar da bincike a kansu domin gano irin rawar da suka taka a ayyukan ta’addanci a yankin.

 

Ko da yake rundunar ba ta fitar da sunayen waɗanda aka kama ba, wani masani kan yaƙi da ta’addanci, Zagazola Makama, ya bayyana sunayen wasu daga cikinsu.

 

Ya bayyana cewa akwai waɗanda suka fito daga ƙauyukan Wawa a Borgu, Gwajibo, Telle, Dukku a Rijau, Pallagi, Arera, Adogon Mallam da kuma Lumma.

 

Wani mazaunin New Bussa ya tabbatar wa Aminiya cewa an kama Alhaji Abdullahi Shehu daga Wawa da wasu mutum biyar daga Lumma.

 

Har yanzu ana ci gaba da bincike domin gano cikakken bayani kan lamarin.

 

 

Mai rahoto

Mustapha Garba Usman

You Might Also Like

Speakers Forum Congratulates Kwara, Katsina Speakers for Securing Governorship, Senate Tickets

Jigawa Governor: Our One Million Votes for Tinubu Are Non-Negotiable , Irreversible

Governor Namadi Affirmed as APC Jigawa State Gubernatorial Candidate for 2027

APC Primaries: Jigawa Speaker Retains Ticket Unopposed

Nursing Mother Inmate Freed as Jigawa NLC Women’s Wing Clears Her Court Fines

Attajdid May 25, 2025 May 25, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
International News

An kai hari asibitin da ake rigakafin shan-inna a Gaza

Attajdid Attajdid November 3, 2024
Firayim Ministan Spain, Pedro Sánchez, ya bayyana cewa ƙasarsa ba za ta ci gaba da hulɗa da Isra’ila ba saboda yadda take ci gaba da kisan al’ummar Falasdinu a Gaza.
WBCD: Jigawa Governor’s Wife Advocates Regular Breast Cancer Screening
Innalillahi wa’innah illahi raji’un Allah ya yima mahaifiyar Tsohun Shugaban Nigeria Rasuwa a yau.
Zanga-zanga ta ɓarke kan zargin sojoji da kashe mata a Adamawa
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?