An kai hari asibitin da ake rigakafin shan-inna a Gaza
Mai Rahoto
Mujahid Muhammad Tasiu
An kai hari kan wani asibitin allurar rigakafin cutar shan inna ta Polio a arewacin Gaza a ranar da aka sake fara aikin rigakafin a can.
Mutane 6 ne suka jikkata, hudu daga cikinsu yara ne.
Jami’an Falasdinawa sun yi zargin cewa jirgin saman Isra’ila maras matuki ne ya kai harin, amma Isra’ila ta musanta hakan.
Hukumar kula da ƙananan yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, ta bukaci Isra’ila da ta gudanar da bincike na gaggawa kan wani hari na daban da aka kai kan wata mota da ke ɗauke da ɗaya daga cikin ma’aikatanta da ke aikin rigakafin a jiya Asabar.




