Amurka ta Gargadi Netanyahu Kada ya Kai Hari
Tashar ta Nukiliya ta Iran
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya tabbatar wa Amurka cewa dakarunsa za su kai hari kan cibiyoyin sojojin Iran, ba tashar makamashin nukiliya ko rijiyoyin man fetur ba bayan da Shugaba Joe Biden ya gargaɗe shi game da kai hari kan tashar ta nukiliya, a cewar wasu rahotanni.
Jami’ai biyu da ba sa so a ambace su, ciki har da wani jami’in Amurka, sun ce Netanyahu ya tabbatar da cewa zai kai hari kan cibiyoyin sojin Iran a wata tattaunawa ta wayar tarho da ya yi da Biden a makon jiya, a cewar jaridar The Washington Post.
Yaƙin da Yahudawan sahyoniyya sun kwashe fiye da shekara ɗaya suna yi a Gaza ya kashe Falasɗinawa aƙalla 42,289. A gefe guda, hare-haren da Isra’ila ta ƙadamar a Lebanon a Oktoban 2023 sun kashe fiye da mutum 2,309 da raba miliyan 1.2 da muhallansu.
At-tajdid News.




