By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Gwamnatin Nijar za ta gina sabuwar matatar man fetur
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Gwamnatin Nijar za ta gina sabuwar matatar man fetur
International News

Gwamnatin Nijar za ta gina sabuwar matatar man fetur

Attajdid
Last updated: 2024/10/27 at 10:48 AM
Attajdid Published October 27, 2024
Share
SHARE

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar da wani kamfanin ƙasar Canada, Zimar, sun sa hannu kan wata yarjejeniya domin gina sabuwar matatar mai a yankin Dosso da ke makwabtaka da Benin.

 

Gwamnatin ta Nijar da kamfanin mai na Zimar sun saka hannu kan wannan yarjejeniya a ranar Alhamis 24 ga Oktoba inda yarjejeniyar ta ƙunshi batun yadda za a tsara aikin ginin matatar da kuɗin da za a kashe wurin ginin da yadda matatar za ta yi aiki da kuma kula da ita bayan kammala gininta.

 

Sabuwar matatar da za a gina a Nijar ɗin ana sa ran za ta rinƙa tace ganga 100,000 a kullum.

 

Mataimakin Shugaban Mulkin Sojin Nijar Salifou Mody wanda shi ne ya bayar da sanarwar ya bayyana cewa wannan aikin zai kasance babbar dama ga Nijar haka kuma sakamakon wannan yarjejeniya da ƙasar ta ƙulla da kamfanin na Canada, ‘yan ƙasar na Nijar za su samu ayyuka da kuma dama iri daban-daban.

 

Mista Mody ya kuma bayyana cewa idan Nijar ta rinƙa tace man da take da shi da kanta, hakan zai taimaka wurin rage dogaro da shigar da mai ƙasar da kuma haɓaka tattalin arziƙin ƙasar.

 

Nijar ta zama ƙasar da ke samar da mai a shekarar 2011 bayan gano mai a Goumeri da Sokor da Agadi da ke yankin Diffa.

 

A Janairun 2012, Nijar ɗin ta ƙaddamar da matatar manta ta farko wadda ke da ƙarfin tace ganga 20,000 a duk rana a yankin Zinder.

 

A watan Janairun bana, ƙasar ta soma fitar da ɗanyen manta zuwa kasuwannin duniya ta hanyar wani bututun mai wanda ke da nisan kilomita 2,000, wanda ya tashi tun daga Nijar ɗin zuwa cikin Benin.

 

Ana kallon wannan matakin da Nijar ɗin ta ɗauka a matsayin ci gaba ta ɓangaren tattalin arziƙinta da kuma rage dogaro wurin shigar da mai cikin ƙasarta.

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid October 27, 2024 October 27, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
International News

Belgium ta bi sahun ƙasashe sama da 140 da suka amince da cin gashin kan Falasɗinu

Attajdid Attajdid September 5, 2025
Ministan Kula da Albarkatun teku Adegboyega Oyetola ya sha Alwashin rage dogaron Nigeria akan shigo da kifi daga kasashen ketare ta hanyar habaka noman kifi a cikin gida tare da kyautata fasahar kiwon kifi a fadin Nigeria.
Jigawa to Create Budget Line for Qur’anic Education to Tackle Out-of-School Children
Hukumar DSS ta saki shugaban Kungiyar Kwadago ta Kasa NLC Ajaero.
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci sojojin Najeriya su ƙara jajircewa wajen yaƙar matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar nan.
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?