Wakiliyar TRT World Zahra Yarali ta rawaito daga garin Fairview na jihar Virginia yadda masu fafutukar goyon bayan Falasdinawa suka fito a rumfunan zabe.
Sun isa rumfunan zabe biyar na yankin DMV (DC, Maryland, Virginia) inda suka rika kira ga masu kada kuri’a su tuna da kisan kare-dangin da Isra’ila take yi wa al’ummar Gaza kafin su jefa kuri’unsu.
Wata Ba’amurkiya ‘yar asalin Falasdinu Hazami Barmada da sauran jama’a sun dauki kwalaye da ke alamta cewa ya kamata mutane su yi zabe na “dimokuradiyya.
An kama wani mutum bayan ya yi mummunar barazana a wata rumfar zabe da ke garin Fowler a birnin New York.
“Bincike ya tabbatar da cewa wani namiji wanda aka taɓa tuhuma da babban laifi ya yi yunkurin kada kuri’a, kuma matsayinsa ya nuna cewa ba shi da rajista tun bayan da aka sako shi daga gidan yari,” in ji sanarwar da rundunar ‘yan sandan jihar ta fitar, inda ta kara da cewa mutumin ya fusata kuma ya fara yin “kalamai masu ban tsoro cewa zai ƙona wurin kuma zai dawo da bindiga.”
‘’Yan sanda sun kaddamar da bincike don neman mutumin, wanda ya gudu daga wurin, amma jim kadan aka kama shi.” Sanarwar ta ce, ana ci gaba da gudanar da bincike.
Ana ta rufe harkokin kasuwanci a yankunan da ke kusa da Fadar White House stare da ɗaukar matakan tsaro yayin da ake taka tsantsan cikin fargabar ɓrkewar rikici a ranar zaben – da kuma kwanaki masu zuwa.
Magajin Garin DC Muriel Bowser ya ce hukumar ‘yan sanda tana kuma ƙara ƙaimi a gundumomin kasuwanci da ke dukkan yankuna takwas na birnin.
Shugabar ‘yan sandan birnin Pamela Smith a wani taron manema labarai ta kuma tabbatar wa mazauna birnin cewa sashenta ya shirya don tunkarar duk wani abu da ranar zabe za ta iya kawowa.
Ta ce, “Tawagarmu ta kasance da cikakkiyar himma da kuma taka tsantsan,” in ji ta. “Mu ne mafi ƙwarewa a kasar nan kan abin da muke yi, kuma za mu ci gaba da aiki ba dare ba rana don kiyaye Washington DC, da kuma kiyaye mazaunanmu.”
TRT Afarka Hausa.
At-tajdid News.




