Amurka ta dakatar da kai wa Isra’ila buldoza 130 domin amfani da su wajen ruguza gidaje a Gaza, kamar yadda jaridun Isra’ila suka ruwaito.
Jaridar Yedioth Ahronoth ce ta ruwaito labarin inda ta ce wasu majiyoyin tsaro sun sanar da ita cewa Amurka ta dakatar da sayar wa Isra’ila buldoza samfurin ‘D9’ wadda kamfannin motoci na Amurka, ‘Caterpillar’ ke kerawa, saboda ana amfani da su domin ruguza gidaje a Gaza, abin da ke jawo ce-ce-ku-ce sosai a Amurka.
At-tajdid News.




