By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Isra’ila ta Kai Sabbin Hare-hare ta Sama a Kudancin Beirut
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Isra’ila ta Kai Sabbin Hare-hare ta Sama a Kudancin Beirut
International News

Isra’ila ta Kai Sabbin Hare-hare ta Sama a Kudancin Beirut

Attajdid
Last updated: 2024/10/21 at 1:20 PM
Attajdid Published October 21, 2024
Share
SHARE

Rundunar sojin Isra’ila ta kai sabbin hare-hare ta sama a Beirut, inda ta fi mayar da hankali a yankunan da ke kudancin wajen babban birnin na Lebanon, bayan Isra’ila ta yi barazanar kai harin bama-bamai kan gine-gine cibiyar harkokin kudi ta Qard al Hassan da ke da alaka da Hezbollah.

 

Jiragen yakin Isra’ila sun kai hare-hare tara cikin awa daya a kan rassan cibiyar da ke Hayy al Sellum, Borj al Barajneh, da kuma Ghobeiry a kudancin Beirut,a cewar kamfanin dillancin labaran Lebanon na National News Agency.

 

Tun da farko, rundunar sojin Isra’ila ta yi barazanar kai hari a “muhimmiyar cibiyar harkokin kudi” ta Hezbollah a Lebanon.

 

Qard al Hassan na daya daga cibiyoyin kudi na Hezbollah, wadda aka kafa a shekarun 1980 domin bayar da sadaka ga al’umma.

 

An kunna jiniyar da ke nuna shiga haɗari mataki na 3, wanda ke nufin matsanancin haɗari a cikin sansanin sojojin tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNIFIL) a garin Maarakeh, gundumar Tyre a kudancin Lebanon.

 

A cewar kamfanin dillancin labarai na Lebanon, an yi gargaɗin ne yayin da barazana take da girma a yankin, yayin da ake ci gaba da artabu da faɗan kan iyaka tsakanin sojojin Isra’ila da ƙungiyoyin yankin.

 

Jami’an UNIFIL da mazauna yankin sun shiga cikin barazana babba yayin da yanayin tsaro a kudancin Lebanon yake ci gaba da taɓarɓarewa.

 

Isra’ila ta yi iƙirarin cewa sojojinta na sama sun kai farmaki kan hedikwatar leƙen asiri ta Hezbollah, da kuma garejin aiki na ƙarƙashin ƙasa inda suke ƙera makamai a Beirut.

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid October 21, 2024 October 21, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

FG To Create One Million Jobs Through SMEs Intervention Vice President Shetima.

Attajdid Attajdid July 23, 2024
SOJOJIN MAMAYA SUN KAI HARI SANSANIN ‘YAN GUDUN HIJIRA NA BALATA.
MAAIKATAN JINYA SUN JANYE YAJIN AIKIN YAU
Pressure Mounts on Sule Lamido To Quiet PDP
Jigawa Border Community Group Flagged-off Tree Planting Campaign To Tackle Environmental Degradation
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?