By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Nijar ta ci gaba da fitar da man fetur ta Jamhuriyar Benin.
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Nijar ta ci gaba da fitar da man fetur ta Jamhuriyar Benin.
International News

Nijar ta ci gaba da fitar da man fetur ta Jamhuriyar Benin.

Attajdid
Last updated: 2024/08/22 at 8:01 AM
Attajdid Published August 22, 2024
Share
SHARE

Nijar ta ci gaba da fitar da man fetur ta Jamhuriyar Benin Wani jami’in kamfanin da ke kula da bututun fetur ɗin Nijar da ya ratsa ta Benin ya tabbatar da cewa wani jirgin ruwa ya yi lodin ɗanyen man fetur ɗin na Nijar kimanin ganga miliyan ɗaya a tekun Benin Rashin jituwa tsakanin Nijar da Benin ya samo asali ne bayan Nijar ta ƙi amincewa ta cire takunkumin da ta saka dangane da haramta shigar da kaya daga Benin.

Hoto: Reuters Nijar ta ci gaba da fitar da man fetur ta Jamhuriyar Benin bayan ƙasashen sun samu matsalar da ta sa aka dakatar da shigar da mai ta hanyar wani sabon bututu da China ta yi aikin shimfiɗawa wanda ya bi ta Benin, kamar yadda kamfanin da ya saka bututun ya sanar a ranar Litinin.

Matsalar da ke tsakanin ƙasashen biyu ta samo asali ne bayan Nijar ta ƙi amincewa ta ɗage takunkumin da ta saka na hana shigo da kayayyaki daga Benin, wanda hakan ya jawo ƙasar ta Benin wadda ke da arziƙin teku ta mayar da martani ta hanyar toshe fitar da man fetur ta ƙasarta a watan Mayu.

A watan Mayu, Nijar ta dakatar da tura mai ta cikin bututun.Wani jami’in kamfanin na West African Gas Pipeline Company (Wapco), wanda ke kula da bututun man, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a ranar Laraba kan cewa wani jirgin ruwa na Aura M ya yi lodin ɗanyen man fetur na Nijar kimanin ganga miliyan ɗaya daga tashar ruwa ta Benin.Bayanai na bin diddigin jiragen ruwa daga MarineTraffic, mai ba da kididdiga kan teku a duniya, sun nuna cewa an loda jirgin kuma ya tashi daga tashar ruwan Benin da yammacin Talata.

TRT AFRIKA.

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid August 22, 2024 August 22, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Sifaniya za ta karɓi tree ministocin ƙasashen Larabawa ranar Lahadi

Attajdid Attajdid May 25, 2025
Sojojin Isra’ila: Sojoji da jami’ai 695 ne aka kashe tun farkon yakin da ake yi a Gaza.
Hukumar Hisbah Ta Kwace Kwalaben Giya 2,400 A Jigawa
Amurka Tana Cigaba Da Taimakwa Isra’ila  Da Makamai Domin Yakar Gaza
Gwamnatin tarayya ta yi gargadin cewa Jahohi guda tara da kuma wasu garuruwa guda 15 a fadin yankin Arewa za su fuskanci mamakon ruwan sama a tsakanin 25 ga watan Augusta zuwa 29 ga watan Augusta wanda kuma ka iya haifar da Ambaliyar ruwa
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?