Kungiyar Hamas ta hannun dakarunta na Kata’ib al-Qassam tare da haɗin gwiwar mayakan Saraya al-Quds ta sanar da kai jerin hare-hare a sassa daban-daban na Yammacin Kogin Jordan da kuma Zirin Gaza. Kungiyoyin sun ce hare-haren sun yi sanadiyyar lalata wasu manyan makaman yaƙi na Isra’ila tare da kashe sojoji.
Sanarwar ta bayyana cewa dakarun Qassam da Saraya al-Quds sun dasa wata babbar nakiya mai ƙarfi a kusa da shingen “Netsani Oz” da ke yammacin lardin Tulkarm, inda suka tarwatsa wata motar soja ta Isra’ila. Kungiyoyin sun bayyana wannan a matsayin wani sabon salo na kai hari daga bangaren Yammacin Kogin Jordan.
A wani bangare na jerin ayyukan da suka kira “Asa Musa” kungiyar Qassam ta saki wani bidiyo da ya nuna yadda aka kai hari kan wata tankin Merkeva a tsakiyar garin Jabaliya, arewacin Gaza.
A bidiyon, wani mai jihadi ya sanya nakiya a cikin ɗakin direban tankin.
Hukumomin Isra’ila sun tabbatar da mutuwar sojojinta hudu a wannan hari, abin da kungiyoyin suka bayyana a matsayin babban nasara.
Qassam ta kuma ce dakarunta sun lalata tankoki biyu na Merkeva da nakiyoyi a yankin Mafraq al-Saftawi, yammacin Jabaliya Camp, a ranar 5 ga Satumba, 2025.
Baya ga haka, a ranar 25 ga Yuli, 2025, kungiyar ta ce ta harbo wata motar daukar sojoji ta Isra’ila da makamin “al-Yasin 105” a yankin al-Satr al-Gharbi, arewacin Khan Yunis.
A nata bangaren, hukumomin sojin Isra’ila sun tabbatar da wasu hare-haren, ciki har da na Jabaliya da ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji, sai dai sun ce suna ci gaba da kai farmaki mai tsanani a Gaza don murkushe kungiyoyin. Gwamnati ta bayyana hare-haren a matsayin “ƙoƙarin tada hankalin jama’a” da kuma “ƙoƙarin rage karfin soja na Isra’ila ba tare da nasara ba”.
Masu lura da harkokin tsaro sun bayyana cewa hare-haren sun nuna yadda kungiyoyin ke ƙara amfani da dabaru masu haɗari da kuma kusantar dakarun Isra’ila kai tsaye. Wasu masana sun ce jerin hare-haren na iya nuna cewa Qassam da abokan hamayyarta na ƙoƙarin ƙara matsa lamba ga Isra’ila a lokaci guda daga Gaza da Yammacin Kogin Jordan.
Mai rahoto;
M.B.S.Gama.
At-tajdid News.




