Ƙungiyar dillalan man fetur a Nijeriya (IPMAN) ta ce ta cimma yarjejeniya da matatar mai ta Dangote, inda yanzu mambobinta za su fara ɗaukar man fetur kai-tsaye daga matatar.
Shugaban Ƙungiyar IPMAN Abubakar Garima ya ce “wannan mataki zai taimaka wajen wadatar man fetur a cikin Nijeriya da kuma samunsa a farashi mai rahusa,” kamar yadda ya shaidawa manema labarai a Abuja ranar Litinin.
A watan jiya ne Alhaji Aliko Dangote ya ce matatarsa tana ajiye da man fetur da ya kai lita miliyan 500 kuma ya yi ƙorafin cewa dillalan man fetur ba sa sayen mansa.
Mai Rahoto;
Zainab Sulaiman Naibawa.
At-tajdid News.




