Mutane sun ɓalle ɗakin ajiyar abinci a Gaza saboda yunwa -WFP
Hukumar abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya, WFP ta ce “wani gungun masu fama da yunwa” ya ɓalle tare da afka wa ɗakin ajiyar kayan abinci a tsakiyar Gaza.
An rawaito cewa mutum biyu sun mutu sannan da dama sun jikkata kuma har yanzu hukumar ta ce tana tattara alƙaluma.
Hotuna sun nuna dubban mutane a lokacin da suke afaka wa ɗakin ajiyar abincin mai suna Al-Ghafari a Deir Al-Balah, inda suka yi awon gaba da buhunan filawa da katan-katan na abinci a daidai lokacin da gunjin bindiga ke tashi.
Ba a samu tabbacin daga ina ne harbin bindigar yake ba.
Hukumar ta WFP ta ce matsalar jinƙai a Gaza ta janyo jama’a sun fita daga hayyacinsu bayan kimanin watanni uku da Isra’ila ta hana shigar da kayan jinƙai Gaza, kafin a sassauta a makon da ya gabata.
Footage showed thousands of people breaking into the Al-Ghafari warehouse in Deir Al-Balah and taking bags of flour and cartons of food as gunshots rang out. It was not immediately clear where the gunshots came from or who fired them.
Mai Rahoto
Mujahid Muhammad Tasiu
AT-TAJDID NEWS




