Gwamnatin Nijar ta saye hannun jarin bankin muslunci na kasar a wani yunkuri na samar da ‘yancin kanta a fannin hada-hadar kudi da bunkasa tattalin arziki.
SIYASAAFIRKA
Nijar ta saye hannun jarin bankin musulunci a Niamey
Gazali Abdou Tasawa
Sa’o’i 11 da suka wuceSa’o’i 11 da suka wuce
Gwamnatin Nijar ta saye hannun jarin bankin muslunci na kasar a wani yunkuri na samar da ‘yancin kanta a fannin hada-hadar kudi da bunkasa tattalin arziki.
A baya dai Babban Bankin Raya kasashen Musulmi na Duniya ne wato BID ke rike da kaso 57 cikin dari a yayin da reshen sa na Bankin tamweel Africa Holding ke mallakar kaso 35 cikin dari na hannun jarin Babban Bankin Muslunci na kasar Nija wanda aka kafa a shekara ta 1983r. To sai dai a yanzu gwamnatin mulkin sojan kasar ta Nija ya saye kaso 95 cikin dari na hannun jarin Bankin Muslunci wanda ya koma a karkashin ikon kasar ta Nijar. Kuma Malam Soly Abdoulahi masalin ilimin tattalin arziki a Nijar ya ce matakin zai taimaka wa Nijar samun ‘yanci a fannin hada-hadar kudi tsakanin bankuna da kuma rage dogaro da wasu bankunan kasa da kasa.
Mai Rahoto
Mujahid Muhammad Tasiu
AT-TAJDID NEWS




