Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa Rt. Hon. Danladi Jatau ya kulle ma’aikatan majalisar dokokin jihar ne, a ranar Larabar da ta gabata saboda rashin komawar ma’aikatan bakin aiki akan lokaci.
Kakakin majalisar wanda ya nuna rashin gamsuwa da rashin nuna halin ko-in-kula na ayyukan ofis, ya gargadi ma’aikatan majalisar kan rashin zuwa bakin aiki yana mai cewa gwamnatinsa ba za ta amince da rashin da’a ba.
Shugaban majalisar ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai, bayan ya zagaya ofisoshi domin duba yadda ma’aikata ke zuwa da kuma lokacin da ake bukata.
Shugaban majalisar wanda yakasance a ofishinsa da misalin karfe 8:30 na safe ya koka da yadda ma’aikatan ke zuwa a makare, inda ya ce majalisa ta 7 da ke karkashin sa ba za ta bari wani ma’aikaci ya yi zagon kasa ga ayyukan majalisar ba.




