By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sauke Shugabannin Riƙo na Kananan Hukumomin Jihar 44
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sauke Shugabannin Riƙo na Kananan Hukumomin Jihar 44
News

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sauke Shugabannin Riƙo na Kananan Hukumomin Jihar 44

Attajdid
Last updated: 2024/09/19 at 8:21 PM
Attajdid Published September 19, 2024
Share
SHARE

Gwamanan ya ɗauki matakin ne wanda ya fara aiki nan take, lokacin da taron ban-kwana da shugabannin na riƙo da aka yi a gidan gwamnatin Kano.

Gwamnan Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya, Abba Kabir Yusuf ya rusa kwamitocin riƙo na ƙananan hukumomin jihar 44, kamar yadda wata sanarwa da kakakin gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ranar Laraba.

Gwamanan ya ɗauki matakin ne wanda ya fara aiki nan take, lokacin taron ban-kwana da shugabannin na riƙo da aka yi a fadar gwamnatin Kano.Sanarwar ta ce an rushe kwamitocin riƙon ne bayan sun cika wa’adin watanni shida da gwamnan ya ba su.

Abba Kabir ya yaba wa shugabannin da aka sauke, yana mai cewa jajiricewarsu ta taimaka wajen taimakon gwamnatin gudanar da kyawawan manufofi.

Gwamnan ya umarci shugabannin da aka sauke su miƙa ragamar tafiyar da al’amura ga daraktocin mulki na kananan hukumomin, har zuwa lokacin da za a zaɓi sababbin shugabanni.

Halaccin shugabannin riƙoA ranar 26 ga watan Oktoba ne hukumar zaben jihar mai zaman kanta za ta gudanar da zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin jihar 44, kamar yadda hukumar ta sanar.Jihar Kano da sauran mafi yawan jihohin ƙasar dai ba su da zaɓaɓɓun shugabanni a matakan ƙananan hukumomi, inda shugabannin riƙo suke jagorantar matakin na gwamnati, wanda ya fi kusa da jama’a.

A watan Yulin 2024 ne Kotun Kolin Nijeriya ta yanke hukuncin cewa naɗa shugabannin riƙo ga ƙananan hukumomi ya saɓa wa doka.

Daga nan ne jihohin ƙasar da dama suka sanar da lokacin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi.

TRT Afarka Hausa.

At-tajdid News.

You Might Also Like

Speakers Forum Congratulates Kwara, Katsina Speakers for Securing Governorship, Senate Tickets

Jigawa Governor: Our One Million Votes for Tinubu Are Non-Negotiable , Irreversible

Governor Namadi Affirmed as APC Jigawa State Gubernatorial Candidate for 2027

APC Primaries: Jigawa Speaker Retains Ticket Unopposed

Nursing Mother Inmate Freed as Jigawa NLC Women’s Wing Clears Her Court Fines

Attajdid September 19, 2024 September 19, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
International News

Mumunan Yajin Aiki Da Zanga-zanga Sun Barke a Isra’ila Domin Nuna Kyamar Ra’ayin Netanyahu.

Attajdid Attajdid September 2, 2024
Court Uphold Engr Auwal As Jigawa  AFAAN Chairman 
PRESIDENT TINUBU APPOINTS CHAIRMAN OF NATIONAL HAJJ COMMISSION
Aljeriya ta Buƙaci Faransa ta Amince ta Aikata Laifuka a Lokacin Mulkin Mallaka
GOV. LAWAL FLAGS OFF CONSTRUCTION OF 200-BED CAPACITY AT TALATA MAFARA GENERAL HOSPITAL, PROCURES ADVANCED MEDICAL EQUIPMENT.
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?