An Rantsar da Fafaroma 14 Leo
An yi bikin rantsar da Fafaroma Leo na 14 a dandalin Saint Peter da ke birnin Vatican a yau Lahadi.
Bikin ya samu halartar dubban mutane, ciki har da shugabannin wasu ƙasashen duniya da suka haɗa da Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky da mataimakin shugaban Amurka, James David Vance da shugaban Najeriya, Bola Tinubu da sauransu.
Wakilin BBC ya ce dubban mutane sun taru a dandalin St Peters, inda ake sa ran Fafaroma Leo zai yi zagaye a cikin motarsu ta Fafaroma.
Tun bayan sanar da sabon Fafaroma ake kwatanta shi da marigayi Fafaroma Francis, ta fuskar zaman lafiya da adalci.
Leo shi ne Fafaroma na 267 kuma na farko da ya fito daga Amurka.
Mai rahoto;
M.B.S.Gama.
At-tajdid News.




