By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: An Sami Mutuwar Mutane 94 a Karamar Hukumar Taura ta Jahar Jigawa Sanadiyar Kwacewar Tankar Mai
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > An Sami Mutuwar Mutane 94 a Karamar Hukumar Taura ta Jahar Jigawa Sanadiyar Kwacewar Tankar Mai
News

An Sami Mutuwar Mutane 94 a Karamar Hukumar Taura ta Jahar Jigawa Sanadiyar Kwacewar Tankar Mai

Attajdid
Last updated: 2024/10/16 at 8:47 PM
Attajdid Published October 16, 2024
Share
SHARE

Hukumomi a Nijeriya sun tabbatar da mutuwar kusan mutum 100 sakamakon gobarar da wata tankar mai ta yi a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin ƙasar.

Tankar ta tashi ne daga jihar Kano a kan hanyarta ta zuwa garin Nguru na jihar Yobe amma ta yi hatsari a yankin ƙaramar hukumar Taura ranar Talata da daddare.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa DSP Lawan Shiisu Adam ya ce mutum aƙalla 94 ne suka mutu sannan fiye da 50 suka jikkata sakamakon gobarar da ta tashi bayan tankar man ta faɗi.

Ya ƙara da cewa lamarin ya faru ne yayin da mutane suke rige-rigen kwasar fetur daga cikin tankar, abin da ya haddasa gobara.

DSP Lawan Shiisu Adam ya ce: “A jiya Talata da misalin 11:30 na dare muka samu labarin hatsarin wata tanka da ta taso daga Kano za ta je Nguru. A lokacin da ta zo Taura kusa da Khadija University, sai motar ta ƙwace daga hannun direban hakan ya sa tankar ta faɗi.

“Sai mai ya riƙa malala yana shiga magudanar ruwa da kwatoci. Wannan dalili ne ya sa mutane sun ga banza ta faɗi suka fito suna ɗiban mai. A lokacin ne wuta ta tashi. A nan-take an samu mutum 94 da wuta ta ƙone su ƙurmus, sai kuma mutum 50 da aka ɗiba aka kai su asibitin garin Ringim inda suke karbar magani,” in ji kakakin ‘yan sandan.

Wasu rahotanni dai su ce mutanen da suka mutu sun zarta 150, kuma ana sa rai adadin zai ƙaru.

Ana yawan fuskantar hatsarin mota a Nijeriya sakamakon tuƙin ganganci da rashin bin dokoki lamarin da kan haddasa asarar rayuka.

At-tajdid News.

You Might Also Like

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

UNICEF Urges Media to Advocate for Increased Water, Sanitation, and Hygiene Budget.

Attajdid October 16, 2024 October 16, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
International News

Gabannin Babban zaben Amurka an kada kuri’ar wuri

Attajdid Attajdid November 3, 2024
Sojojin  Isra’ila Sun Kai Hari Makarantar Salah al-Din a Take Gaza
Yan Bindiga Suka kashe Wani Dan Takarar kamsila..
GOVERNOR DAUDA LAWAL @ 59:
BREAKING: Ex-US President Donald Trump escapes assassination attempt [Video]
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?