By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Kwamitin Binciken Zanga-zangar Matsin Rayuwa A Kano Zai Bayar Da Rahotansa Cikin Watanni 3
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Kwamitin Binciken Zanga-zangar Matsin Rayuwa A Kano Zai Bayar Da Rahotansa Cikin Watanni 3
News

Kwamitin Binciken Zanga-zangar Matsin Rayuwa A Kano Zai Bayar Da Rahotansa Cikin Watanni 3

Attajdid
Last updated: 2024/09/05 at 9:06 PM
Attajdid Published September 5, 2024
Share
SHARE

Kwamitin da gwamnatin jahar Kano, kafa don bincikar abubuwan da suka faru a zanga-zangar matsin rayuwa, wadda ta haifar da tarzoma, ya ce zai gudanar bincike kan dalilin da sanya hakan ta faru, da wadanda suka yi aika-aikar da masu taimaka mu su, da suka hadar da kungiyoyi da kuma daidaikun jama’a .

Shugaban kwamitin Justice Lawan Wada, mai ritaya ne ya bayyana hakan, a taron manema labarai da aka gudanar ayau Alhamis 5 ga watan Satumba 2024 a birnin Kano.

Zanga-zangar wadda aka gudanar a watan augustan 2024, inda rikide zuwa tarzoma, har aka yi asarar rayuka, dukiya da kuma kone-kone a wasu sassan birnin Kano.

A cewar kwamitin binciken da za su gudanar , shi ne zai tabbatar da hakan, tare da kiyasta kimar dukiyar da aka rasa.‘’don haka za mu bi guraren da muna da niyar za mu bi wuraren da muka tabbatar an yi wadannan abubuwa za muje, mu gani da idon mu da kuma karbar abubuwan da suka rasa’’ cewar Justice L.Wada’’.

Idongari.ng, taruwaito cewa, gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ne ya umarci kwamitin da zai binciken kan  tarzomar da aka yi lokacin zanga-zangar matsin rayuwa a jihar, da kada su sassautawa duk wanda aka samu da laifi.

Kwamitin ya ziyarci babbar kotun jahar Kano dake sakatariyar Audu Bako da kuma ma’aikatar Dab’I ta jahar Kano don ganin barnar da aka yi, a lokacin gudanar da zanga-zangar.

Haka zalika Justice L. W. Muhammed , ya kara da cewa suna fatan jama’a za su taimakawa kwamitin wajen kawo mu su labarin irin abubuwan da suka faru ba tare da jin tsoro ba.

idan al’umma ba su kawo mana labarin abinda ya faru ba babu abinda za mu iya yi’’cewar sa’’.

Ya kuma roki yan jarida da su fadakar da al’umma don suje su bayar da bayanai, ba tare jin tsoron komai ba, tunda dai doka ce ta kafa kwamitin kuma za su kare mutuncin kowa da hakkinsa.

Kwamitin ya kara da cewa a bangaren su za su yi adalci, bisa abubuwan da suka fahimta ba tare da fargaba ko shakkar kowa ba.Ya kuma tabbatar wa da al’ummar jahar Kano cewa, babu wani jami’in gwamnati da zai tsoma mu su baki kamar yadda  gwamnan jahar Abba Kabir Yusuf ya tabbatar mu su.

Kwaimitin dai yana saran karbar shawarwari daga malamai, sarakuna, Dattawa don daukar matakin dakile faruwar hakan anan gaba.Idongari.ng, ta ruwato cewa kwamitin zai kammala aikinsa ne cikin watanni uku, don mika rahotansa kan abubuwan da suka faru.

Idan ba a manta ba wasu Bata-gari sun far wa ofishin Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) da ke Kano inda suka kwashe kwamfutoci da kujeru wasu kayan aiki masu tarzomar sun kuma cinna wuta a ofishin, da kuma shiga babbar kotun jahar Kano dake sakatariyar Audu Bako,kafin daga bisani jami’an tsaro su kawo dauki a wurin.

Haka zalika an farfasa manya da kananan shagunan siyar da kayan abinci, tare da yin awon gaba da su, sai dai suma jami’an tsaro sun yi nasarar kama wa da kuma dawo da wasu daga cikin kayan da aka sace.

Mai rahoto;Salihu Garba.

At-tajdid News.

You Might Also Like

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

UNICEF Urges Media to Advocate for Increased Water, Sanitation, and Hygiene Budget.

Attajdid September 5, 2024 September 5, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Burkina Faso da Senegal za su ƙulla alaƙar tsaro

Attajdid Attajdid May 17, 2025
Kotu ta ci su El-Rufa’i tarar miliyan 900
Ɗantakarar Hamayya ya Kayar da Shugaban ƙasa Mai-ci a Somalilan
Gwamnan Jihar Neja Mohammed Umaru Bago, ya bayyana tsohon Shugaban Mulkin Soja Ibrahim Badamasi Babangida a matsayin wani fitila kuma abin koyi ga takwarorin sa da dama, yana mai cewa tarihi zai ci gaba da tunawa da gudummawar da ya bayar
2027: Tinubu’s Continuety Posters Floods Jigawa
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?