Mataimakin Shugaban Nijeriya Kashim Shettima wanda ya wakilci shugaban ƙasar Bola Tinubu ya ƙaddamar da Gasar Wasannin Sojoji ta Ƙasashen Afirka karo na biyu a Abuja babban birnin ƙasar a ranar Laraba.
Za a gudanar da gasar wasannin ne har zuwa 30 ga watan Nuwamba.
Gasar ta bana ta samu baƙuncin ƙasashe waɗanda suka haɗa da Ghana da Kamaru da Senegal da Aljeriya da sauransu. Haka kuma za a gudanar da wasanni iri daban-daban har guda 19 a gasar ta bana.
Mai Rahoto;
Zainab Sulaiman Naibawa.
At-tajdid News.




