By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Mutum Uku ke Magana da Yawuna Tinubu Shugaban Najeriya, Bola Tinubu
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Mutum Uku ke Magana da Yawuna Tinubu Shugaban Najeriya, Bola Tinubu
News

Mutum Uku ke Magana da Yawuna Tinubu Shugaban Najeriya, Bola Tinubu

Attajdid
Last updated: 2024/11/19 at 1:37 PM
Attajdid Published November 19, 2024
Share
SHARE

Mutum Uku ke Magana da Yawuna Tinubu

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu

 

 

Bayanan hoto,Shugaban Najeriya, Bola Tinubu

Fadar shugaban Najeriya ta ce shugaba Tinubu ya yi garambawul game da ayyukan jami’ansa da ya naɗa a sashen hulɗa da kafafen yaɗa labaru, domin bunƙasa ɓangaren.

 

Wata sanarwa da mai taimaka wa shugaba Tinubu kan yaɗa labaru da tsare-tsare, Bayo Onanuga ya fitar ta ce a yanzu dukkanin mutane uku da aka naɗa a muƙaman yaɗa labaru za su zamo masu magana da yawun shugaban ƙasa.

 

Sai dai sanarwar ta ce Mista Sunday Dare a yanzu shi ne mai bai wa shugaban ƙasar shawara na musamman kan kafafen yaɗa labaru da hulɗa da jama’a.

 

Haka nan Mista Daniel Bwala, wanda a makon da ya gabata aka bayyana a matsayin mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan kafafaen yaɗa labaru da sadarwa yanzu zai riƙe muƙamin mai bayar da shawara na musamman kan yaɗa manufofin gwamnati.

 

Sanarwar ta ce idan aka yi la’akari da cewa akwai kuma Bayo Onanuga, wanda shi ne mai taimaka wa shugaba Tinubu kan yaɗa dabarun gwamnati “za a ga cewa babu mutum ɗaya tilo da ke riƙe da muƙamin mai magana da yawun shugaban ƙasa”.

 

“Saboda haka dukkanin mashawartan na musamman uku za su zamo masu magana da yawun gwamnati.”

 

An dade dai ana raɗe-radin cewa akwai rashin jituwa a ɓangaren masu taimaka wa shugaba Tinubu kan yaɗa labaru, inda ayyukan wasu jami’an ke shiga cikin na wasu.

 

A cikin watan Satumban da ya gabata ne, mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Nagelale ya ajiye muƙaminsa ‘bisa wasu dalilai na ƙashin kai’ kamar yadda ya bayyana.

 

Sai dai kafafen yaɗa labaru da dama sun yi bayanin cewa ajiye muƙamin nasa ba zai rasa nasaba da rashin jituwar da ke tsakanin jami’an da shugaba Tinubu ya naɗa a ɓangaren yaɗa labarun na fadar shugaban ƙasa ba.

 

Mai Rahoto;

Mujahid Muhammad Tasiu.

 

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Nursing Mother Inmate Freed as Jigawa NLC Women’s Wing Clears Her Court Fines

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

Attajdid November 19, 2024 November 19, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
International News

‘Isra’ila ta amince da shawarar tsagaita wuta a Gaza

Attajdid Attajdid May 29, 2025
Ten Injured, APC Secretariat Burnt.
Isra’ila Ta Kaddamar Da Hari a Yammacin Kogin Jordan Na PalastinuIsra’ila ta gaddamar da hari a arewa maso yammacin kogin Jordan
An sake kama fursunoni 51 da suka tsere daga gidan yarin Maiduguri
Fafaroma Francis ya Nemi Ayi Bincika ko Isra’ila na aikata Kisan Kiyashi a Gaza
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?