A yau Yahudawan sahyoniya sun Kashe Mutane Fiye da 50 da ya Hada da Kanan Yara a Gaza
Cikin wani saƙo da aka wallafa daga Gaza Now, an jaddada girman halin ƙuncin da al’ummar Gaza ke ciki, inda aka ce: “Wataƙila wasu su ɗauka cewa gudummawa kaɗan ko kalmar ta’aziyya ba za su kawo sauyi ba, amma gaskiya muna buƙatar komai. Ko kalma mai kyau tana iya haskaka mana cikin wannan duhu. Mutanen Gaza na buƙatar ku, ku kasance tare da su da tallafi.”
A gefe guda kuma, jiragen yaƙin Isra’ila sun kai hari ta sama a birnin Khan Younis da ke kudancin Gaza, inda suka nufi ƙungiyar yara, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar wasu daga cikinsu.
Haka kuma, sojojin Isra’ila sun kai hari da manyan bindigogi a titin Al-Qayidh da ke cikin unguwar Sabra a kudu da birnin Gaza, inda aka tabbatar da mutuwar mutane bakwai (7) tare da raunata wasu da dama.
Rahotanni sun nuna cewa jimillar mutane 50 ne suka mutu sakamakon hare-haren Isra’ila a kan Zirin Gaza a wannan rana.
Bugu da ƙari, mutane 10 sun mutu yayin da suke jiran agaji a yankin As-Sudaniya da ke arewa maso yammacin Gaza.
Mai rahoto;
M.B.S.Gama.
At-tajdid News.




