By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Sojojin Nijeriya Shida da ‘Yan Boko Haram 34 Sun Mutu a Wata Arangama a Borno
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Sojojin Nijeriya Shida da ‘Yan Boko Haram 34 Sun Mutu a Wata Arangama a Borno
News

Sojojin Nijeriya Shida da ‘Yan Boko Haram 34 Sun Mutu a Wata Arangama a Borno

Attajdid
Last updated: 2025/01/08 at 3:22 PM
Attajdid Published January 8, 2025
Share
SHARE

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kashe ‘yan ta’adda 34 a wani artabu da suka yi da ‘yan Boko Haram a arewa maso gabashin jihar Borno sannan kuma sojoji shida sun mutu.

 

Rikicin ya faru ne a kauyen Sabon Gari lokacin da ‘yan ta’addan suka yi wa sojojin da ke komawa sansaninsu kwanton bauna, kamar yadda kakakin rundunar, Manjo-Janar Edward Buba ya bayyana a ranar Laraba.

 

Ya ce ‘yan ta’addan na kungiyoyin Boko Haram da ISWAP ne. Suna tafiya ne a kan babura da manyan motoci dauke da bindigogi lokacin da suka kai harin a ranar Asabar.

 

Dakarun tare da taimakon wasu dakaru na rundunar sa kai na Civilian Joint Taskforce da kungiyoyin ‘yan banga sun yi nasarar dakile harin, in ji shi.

 

Nijeriya dai ta shafe shekaru 16 tana fama da tashe-tashen hankula a yankin arewa maso gabashin kasar da kungiyar Boko Haram ke haddasawa da kuma kungiyar ta ISWAP, wanda ya janyo asarar dimbin jama’a da na tattalin arziki da suka hada da gudun hijira da kuma matsalar jinƙai.

 

Buba ya ce sojoji 6 ne suka mutu a harin arangamar da wasu bama-bamai da aka dasa suka tashi suka raunata kwamandan ‘yan banga.

 

Hakazalika rundunar sojin saman Nijeriya ta kai farmaki ta sama kan ‘yan ta’addan da suka tsere, lamarin da ya yi sanadin jikkatar mutane 34 da aka kashe a rikicin, in ji Buba. TRT Africa Hausa.

 

 

Mai rahoto;

M.B.Gama.

 

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Nursing Mother Inmate Freed as Jigawa NLC Women’s Wing Clears Her Court Fines

NASSI Hails Governor Namadi’s Progressive Policies for Small Businesses

Ramadan Feeding: Jigawa Plans to Put 8 Million Meals on the Tables of the Need

RT Hon Dangyatin Emerged Chaiman Progressive Speakers Conference

Jigawa Appoints Emir Of Dutse As 2026 Amirul Hajji

Attajdid January 8, 2025 January 8, 2025
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Jigawa Declares Free Medical Treatment For Livestock In an effort to enhance food security, boost the rural economy, and improve animal husbandry practices.

Attajdid Attajdid September 28, 2024
Gwamnan Kano Eng. Abba Kabir ya Bara Kan Rade-raden Sabani Tsakaninsa da Jagoran Jam’iyyar NNPP
Mutum 25 Sun Rasu Bayan Bullar Sabuwar Annoba a Jahar Sokoto
Mun kashe Halilu Sububu saura Bello Turji da Sauran ‘ƴan Ta’adda
Ƴanbindiga sun cinna wa gonaki wuta a jihar Zamfara
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?