Tsohon Shugaban Amuruka Ya Kamu Da Cutar Daji
Likitoci sun tabbatar da tsohon shugaban Amurka, Joe Biden ya kamu da ciwon Daji ( Cancer )
Sakamakon wasu gwajegwaje da aka yiwa tsohin Shugaban an gano yana dauke da cutar daji a kwarkwaron mazakutarsa wadda ta kai ga bazuwa har zuwa kasusuwa.
Wannan cuta, cuta ce mai haɗari, za’a iya maganin ta, ta hanyar samar da wasu sinadarai wato hormone a jiki, yayinda shi da iyalinsa su ka fara nazarin hanyoyin magance matsalar.
Shugaba Donald Trump da yar takarar shugabancin ƙasa a zaɓen 2024, Kamala Harris, sun taya shi addu’a da fatan samun sauki.
Wannan ciwo ya fito bayan Biden ya janye daga takarar shugabancin Amurka na 2024 saboda matsalolin lafiya da shekarunsa.
Muazzam Hamza
AT-TAJDID NEWS




