Kasar China Tana Yunkurin Rusa Wani Masallaci Tare Muzgunawa Musulman Kasar
Duk da kokarin su wajen tabbatar da dorewar zaman lafiya a tsakanin al’ummomin China, mazauna unguwar sun yi zaman hakuri a tsawon shekaru da aka shafe ana wahalar zaman rayuwa a yankin.
Al’ummar Musulmai masu rinjaye a garin Hui da ke yankin kudu maso yammacin China sun yi wata arangama da ‘yan sanda, lokacin da aka yi yunkurin rusa wani masallaci, a wani mataki na nuna iko a kan addini da jam’iyyar Kwaminisanci ke yi.
A tsawon shekarun da suka gabata, Beijing ta yi ta kokarin aiwatar da tsarin “sauya fuskar addinai” – wato wani yunkuri na sauyawa ‘yan China addinansu, musamman na Musulunci.
Ana ganin matakin zai rage tasirin da addinai ke da shi a kan mutane domin samun damar karfafa al’adar kasar da tsarin Jam’iyyar Kwaminisanci a kansu.
A tsakanin gwaje-gwajen da aka yi ta gudanarwa, akwai kabilu da dama daga lardin Najiaying da keYunnan, wani yanki da ya hada iyakar China da kudu maso gabashin Asia, mai dauke da mabiya addinai mabanbanta.
A ranar Asabar ne, gomman jami’an ‘yan sanda rike da faranti da hular kare kansu, suka bi kan dandazon mutanen da suka taru a gaban Masallacin Najiaying, kamar yadda hotuna da bidiyoyi da suka karade shafukan sada zumunta suka nuna, da kuma bayanai daga shaidun gani da ido.
Mutane da dama ne jami’an ‘yan sandan suka kama biyo bayan lamarin da ya faru, kazalika an jibge daruruwan jami’an tsaro a cikin garin tun daga ranar Litinin, a cewar wasu shaidu biyu.
“Masallaci tamkar gida ne ga Musulmai, idan suka yi yunkurin rusa shi, tabas ba za mu bari su yi hakan ba,” a cewar wata mazauniyar garin a hirarta da kamfanin dillancin labarai na AFP.
Mai rahoto;
Mustapha Garba Usman.
At-tajdid News.




