Cibiyar tallafawa harkokin kasuwanci ta ƙasa CPPE, ta gargadi cewa ci gaba da hauhawar farashin abinci da kuma tsadar kaya na nuna cewa har yanzu akwai matsalolin tsarin tattalin arziki da ba a magance ba, duk da saukar da aka samu a kan babban hauhawar farashi a baya-bayan nan.
Daraktan kuma babban jami’in gudanarwar cibiyar, Dr Muda Yusuf, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi yana jaddada cewa rahoton hauhawar farashin watan Yuli 2025 ya nuna sakamako mai sauyawa, wanda ya bukaci a yi taka-tsantsan tare da ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki.
Ya bayyana cewa, hauhawar farashin ya ragu karo na hudu a jere, inda ya sauka daga kashi 22.22 cikin ɗari a watan Yuni zuwa kashi 21.88 cikin ɗari a watan Yuli.
Hauhawar farashin abinci daga wata zuwa wata ma ya dan lafa, daga kashi 3.25 cikin ɗari a Yuni zuwa kashi 3.12 cikin ɗari a watan Yuli, yayin da asalin hauhawar farashin ya nuna kankanin sauki da aka samu a shekara.
Yusuf ya lura cewa wannan ci gaba mai kyau na nuna daidaituwar yanayin tattalin arziki a hankali, wanda ya samu goyon bayan daidaituwar kudin musaya, ƙarin kwarin gwiwar masu zuba jari, da kuma sassauta harajin shigo da kayayyakin abinci kamar shinkafa, masara da dawa. Ya kara da cewa tasirin kwatankwacin farashin shekaru da suka gabata, bayan tsananin hauhawar farashi a shekarar 2022, shi ma ya taimaka wajen saukar da farashin.
A gefe guda kuma, rahoton jaridar The PUNCH ya bayyana cewa shirin da Kamfanin Mai na Dangote ya tsara na fara rarraba man fetur ta amfani da manyan motocin gas guda 4,000 ya samu tsaiko sakamakon matsalar harkar sufuri daga kasar Sin da ta jawo rashin jigilarsu a kan lokaci.
Kamfanin da ya kai darajar dala biliyan 20 da ke Lekki, tun da farko ya sanar da shirinsa na kaddamar da rarraba man fetur kai tsaye da wadannan manyan motocin gas 4,000 da aka yi odarsu daga kasar Sin domin a kawo su Lagos don fara aikin rarraba man Dangote.
Sai dai shirin bai tabbata ba domin kamfanin ya karɓi motoci 450 kacal zuwa yanzu. An samu labarin cewa wasu motocin 150 za su iso mako mai zuwa, wanda zai kai adadin motocin zuwa 600.




