By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Da Alama Za a Kwashe Shekaru Masu Yawa Ana Yaki a SudanYaƙin Sudan.
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > International News > Da Alama Za a Kwashe Shekaru Masu Yawa Ana Yaki a SudanYaƙin Sudan.
International News

Da Alama Za a Kwashe Shekaru Masu Yawa Ana Yaki a SudanYaƙin Sudan.

Attajdid
Last updated: 2024/08/25 at 12:08 PM
Attajdid Published August 25, 2024
Share
SHARE

ya raba miliyoyin mutane da muhallansu, inda dubbai suka yi gudun hijira zuwa ƙasashen maƙota, yayin da aka kashe dubbai.Dakarun sojin Sudan ƙarƙashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan sun kwashe watanni 16 suna fafatawa da mayaƙan rundunar kai ɗaukin gaggawa ta Rapid Support Forces.

Shugaban mulkin sojin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, ya ce gwamnatinsa ba za ta shiga tattaunawar zaman lafiya da ake yi a Switzerland ba da rundunar kai ɗaukin gaggawa ta ƙasar, yana mai cewa maimakon haka za su kwashe “shekara 100 suna yaƙi.”

“Ba za mu je Geneva ba… za mu kwashe shekara 100 muna yaƙi,” in ji Burhan, wanda dakarunsa suka kwashe watanni 16 suna fafatawa da mayaƙan rundunar kai ɗaukin gaggawa ta Rapid Support Forces.

Ya bayyana haka ne ga manema labarai ranar Asabar a Port Sudan.Amurka ta buɗe wani shirin tattaunawa a Switzerland ranar 14 ga watan Agusta da zummar kawo ƙarshen bala’in da yaƙi ya jefa ƙasar ta Sudan.

Wakilan RSF sun halarci wurin tattaunawar, sai dai gwamnatin Sudan ba ta amince da tsarinsa ba, kuma ba ta je wurin taron ba, ko da yake ta yi magana ta wayar tarho da masu shiga tsakani.Saudiyya da Switzerland, da Tarayyar Afirka da Masar da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Majalisar Ɗinkin Duniya na cikin mahalarta taron wanda ke neman samar da dawwamammen zaman lafiya a Sudan.

Sun kammala taron ranar Juma’a ba tare da cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta ba ko da yake an samu ci gaba game da shigar da kayan agaji ƙasar ta wasu muhimman hanyoyi.

Yaƙin Sudan ya raba miliyoyin mutane da muhallansu, inda kimamin mutum miliyan 25 a faɗin ƙasar suke fama da bala’in yunwa.

At-tajdid News.

You Might Also Like

Mass Turnout As Jigawa Flagg-Off 2025 Polio Immunization Campaign Targets 1.5 Million Children 

ZAMFARA STATE MUSLIMS LEAGUE FOR PEACE AND DEVELOPMENT OPEN LETTER TO TRUMP AND THE U.S.A CONGRESS:

Israel Strategies For Dividing Gaza Intro Two Zone

⭕️ Reuters, citing European and American sources

Israila ta Rushe Gidajen Falasɗinawa a Gaza, ta ƙaddamar da Sabon Hari a Khan Younis

Attajdid August 25, 2024 August 25, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
News

Ana Cigaba Kashe ‘Yan Jaridu a Gaza Sakamakon Harin Yahudawan Sahyoniya a Gaza

Attajdid Attajdid August 25, 2025
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya bayar da gudunmawar kudi kimanin Naira miliyan 5 da fili ga kowanne daga cikin iyalan ‘yan wasa 22 da suka rasu
Gwamnatin Kano ta haramta bikin ‘ƙauyawa day’ da soke lasisin gidajen bukukuwa
A Leap Forward: Governor Namadi’s Vision for Jigawa’s Youth
NNPCL Ya Kara Farashi Fetur Daga N620 Zuwa  N897
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?