By using this site, you agree to the Privacy Policy and Terms of Use.
Accept
At'tajdid NewsAt'tajdid NewsAt'tajdid News
Notification Show More
Font ResizerAa
  • News
    • International News
  • Video
  • Lecture Audio
    • Tafsir
  • More
    • Books & Journal
      • Feature/Articles
    • Contact
    • Search Page
    • Blog
    • About Us
Reading: Bambam Bakin Nigeria CBN Ya Tabbatarwa Da ‘Yan Kasa Kudadansu Suna Cikin Aminci
Share
Font ResizerAa
At'tajdid NewsAt'tajdid News
  • HomeHome
  • My Feed
  • My Interests
  • My Saves
  • History
  • Blog
Search
  • Quick Access
    • Home
    • Contact Us
    • About Us
  • Categories
    • News
    • International News
    • Video
    • Books & Journal
    • Feature/Articles
    • Lecture Audio
    • Tafsir
Have an existing account? Sign In
Follow US
At'tajdid News > Blog > News > Bambam Bakin Nigeria CBN Ya Tabbatarwa Da ‘Yan Kasa Kudadansu Suna Cikin Aminci
News

Bambam Bakin Nigeria CBN Ya Tabbatarwa Da ‘Yan Kasa Kudadansu Suna Cikin Aminci

Attajdid
Last updated: 2024/10/08 at 5:05 PM
Attajdid Published October 8, 2024
Share
SHARE

 

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya tabbatarwa da ‘yan Nijeriya cewar kar su firgita inda bankin ya tabbatar da cewar dukkan kudaden da aka ajiye a bankunan kasar na nan kalau.

 

Sanarwar da mukaddashin daraktar ayyuka na Babban Bankin Hakama Ali ta fitar a ranar Talata ta sake tabbatarwa da jama’a kan ayyukan da suke yi na tabbatar da zaman lafiya da daidaito a bankunan Nijeriya.

 

Wannan cigaba na zuwa ne a yayin da jama’ar kasar a ranar Litinin suke ta raɗe-raɗi da gargadin kwastomomi su kwashe kudadensu daga wasu bankunan sakamakon ƙwace lasisinsu da babban bankin ya yi.

 

Sanarwar ta ce “CBN na ayyukan tabbatar da cewa bankuna sun yi aiki da ka’idojin aikin banki don tabbatar da gaskiya a tsarin ta’ammali da kudade.

 

“Ana yawan gudanar da bincike da gwaji don gano wane rauni da ake da shi, don taimakawa a tabbatar da ƙarfafuwar hukumomin kuɗaɗenmu.”

 

“Dadin daɗawa, CBN din ya aiwatar da tsarin gargadi da wuri da ke riga malam masallaci wajen gani wani hatsari tare da magance shi, wanda ke ba mu damar kawar da duk wata matsala da aka gano a kan lokaci.”

 

“Tsarin Bankin na Sanya Idanu Kan Yiwuwar Fadawa Hatsari na tabbatar da an mayar da hankali ga dokokin da aka kafa wa hukumomin kudi da za su iya kawo wani hatsari ga sha’anin kudi a kasar.

 

“Wannan aiki na bayar da dama wajen samar da kyakkyawan tsari tare da habaka sahihancin bankunan.”

 

Haka zalika, CBN ya bayyana kulla yarjejeniyar fahintar juna da kasashe da dama da bankunan Nijeriya ke da rassa.

 

“Wannan hadin kai na inganta aiki da dokoki da tabbatar da bankunanmu sun yi aiki a karkashin dokokin aikin baki, a cikin gida da kasashen ketare”

 

Sanarwar ta kuma ce “CBN na mayar da hankali don samar da tsarin bankuna mai tsaro da inganci inda masu ajiya za su amince da ajje kudadensu.

 

“Bankin zai ci gaba da sanya idanu da tabbatar da aiki da ka’idoji don kare martabar dukkan masu ta’ammali da kudade da bayar da kariya ga tsarin bankinmu.”TRT Afarka Hausa.

 

At-tajdid News.

You Might Also Like

Speakers Forum Congratulates Kwara, Katsina Speakers for Securing Governorship, Senate Tickets

Jigawa Governor: Our One Million Votes for Tinubu Are Non-Negotiable , Irreversible

Governor Namadi Affirmed as APC Jigawa State Gubernatorial Candidate for 2027

APC Primaries: Jigawa Speaker Retains Ticket Unopposed

Nursing Mother Inmate Freed as Jigawa NLC Women’s Wing Clears Her Court Fines

Attajdid October 8, 2024 October 8, 2024
Share This Article
Facebook Twitter Email Print
Leave a comment

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Follow US

Find US on Social Medias
Facebook Like
Twitter Follow
Youtube Subscribe
Telegram Follow

Weekly Newsletter

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

Popular News
International News

Gabannin Babban zaben Amurka an kada kuri’ar wuri

Attajdid Attajdid November 3, 2024
Sojojin Nijeriya Shida da ‘Yan Boko Haram 34 Sun Mutu a Wata Arangama a Borno
Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Wadanda Aka Samu Da Laifin Satar Bindiga Da Siyar Da Ita
TAI da Baykar na Turkiyya na daga cikin manyan kamfanonin ƙera jiragen sama 50 na duniya
Makomar Najeriya na hannun matasa
- Advertisement -
Ad imageAd image
Global Coronavirus Cases

Confirmed

0

Death

0

More Information:Covid-19 Statistics

Categories

  • U.K News
  • Today News
  • Hot News
  • Video

About US

Attajdid News, a Nigerian media outlet, is dedicated to fostering dialogue among diverse communities, promoting integrity, transparency, and critical thinking.

Subscribe US

Subscribe to our newsletter to get our newest articles instantly!

© Foxiz News Network. Ruby Design Company. All Rights Reserved.
Welcome Back!

Sign in to your account

Lost your password?