Rahotan Yadda Aka Wayi Gari a Yankin Gaza
Gaza Now ta ruwaito cewa al’amura sun kara tsananta a cikin Zirin Gaza yayin da hare-haren Isra’ila ke ci gaba da jefa fararen hula cikin mawuyacin hali.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi mummunar kisan gilla a cikin sansanonin ‘yan gudun hijira, inda mutane da dama suka mutu tare da samun raunuka sakamakon hare-haren da dakarun Isra’ila suka kai.
A arewacin Gaza, a wajen rabon tallafin abinci a Zikim, daruruwan fararen hula da ke fama da yunwa sun hallaka yayin da suke cikin jerin neman abinci, bayan harin da sojojin mamaya suka kai musu.
Haka kuma, gidajen jama’a sun ci gaba da rushewa, lamarin da ya tilasta dubban mutane kafa tantuna a bakin tekun Gaza, a karkashin mawuyacin yanayi na yunwa da talauci.
A wajen Gaza kuwa, al’ummar Mexico sun gudanar da zanga-zangar adawa da kisan kiyashi, inda suka kai farmaki suka kona safarar Isra’ila a Mexico City, a matsayin martani ga abin da suka kira laifukan yaki da yunwar da ake jefa Falasdinawa a ciki.
Daga cikin Gaza kuma, rahotanni sun bayyana yunkurin ceto wani karamin yaro da ya samu raunuka sakamakon harin da Isra’ila ta kai a yankin al-Karama da ke arewacin Gaza.
Mai rahoto;
M.B.S.Gama.
At-tajdid News.




