Matatar man Isra’ila ta daina aiki bayan sabon harin Iran.
Tue, 17 Jun 2025 10:17:39 GMT+0100
Matatar man ƙasar Isra’ila dake yankin Haifa ta dakatar da ayyukanta gaba daya bayan hari da Iran ta kai mata.
Hukumar gudanarwar matatar man ƙasar Isra’ila dake yankin Haifa ta sanar da cewa matatar ta dakatar da ayyukanta ɗungurungum bayan harin da Iran ta kai mata.
Kamfanin Bazan Group dake kula da matatar ya ce harin na Iran ya tilasta musu tsayar da gaba ɗaya — a yayin da sabon rikicin na yankin Gabas ta Tsakiya ke ɗaukar zafi tsakanin ƙasashen biyu da suka jima suna yi wa juna kallon hadarin kaji.
Bazan Group ya bayyana cewa, harin rokokin Iran ya lalata tashar wutar lantarki da matatar ke amfani da shi.
Harin na Iran ya kuma halaka ma’aikata uku a matatar ta Haifa, kamar yadda hukumomin Isra’ila suka sanar.
Wannan na faruwa a ci gaban hare-haren ramuwar gayya da makamai masu linzami da Iran ke kaiwa, bayan jiragen Isra’ila sun ƙaddamar da hare-hare da kawo yanzu suka yi ajalin mutane sama da 220 a sassan Iran, har da Tehran, Babban birnin ƙasar.
Kashi 70 na mutanen da Isra’ila ta kashe a Iran mata da ƙananan yara ne; da wasu manyan jami’an tsaro da wani masanin kimiyyar makamashin nukiliya.
Majiyar mu ta ruwaito Isra’ila na cewa ta ƙaddamar da hare-haren ne domin daƙile Iran, wadda ke dab da mallakar makamin nukiliya a cikin wannan shekara, ko cikin watanni kaɗan masu zuwa.
Ana iya tuna cewa Firaiminista Banjamin Netanyahu ya bayyana cewa hallaka shugaban addinin Iran, Ayatullah Khamene’i zai yi tasiri wajen kawo karshen rikicin.
A nata bangaren Iran ta bayyana cewa Isra’ila za ta yabawa aya zaƙinta, kan waɗannan hare-haren ragoncin da ta kai wa fararen hula da cibiyoyin soji da tashoshin makamashin nukiliyarta.
Ta kuma bayyana harin bai tsayar da shirinta na nukiliya domin samar da wutar lantarki da sauran abubuwa na zaman lafiya ba.
Ramuwar gayyar Iran ta shafi cibiyoyin sojin Isra’ila da tashar wutar lantarki da matatar mai, baya ga halaka mutane sama da 24 da lalata gine-gine a wurare daban-daban, ciki har da birnin Kudus, da kuma Tel Aviv, babban birnin ƙasar Isra’ila.
Mai rahoto
Mustapha Garba Usman
At’tajdid News




